Iraniyawa da musulman duniya sun yi taron tunawa da wafatin Imam Khomeini
Jagoran juyin-juya halin musulunci a Iran, marigayi Ayatollah Ruhollah Mosavi Khomeini, wanda aka fi sani da Imam Khomeini.
'Yan kasar Iran, musulmai da sauran masu neman 'yanci a fadin duniya sun yi taron tunawa da wafatin Imam Khomeini, jagoran juyin-juya halin musulunci a ranar 4 ga watan Yuni.
Rana ta 14 ga Khordad a kalandar Iran itace ranar tunawa da wafatin jagoran Jamhuriyar Musulunci, Ayatollah Ruhullah Mosavi Khomeini, wanda aka fi sani da Imam Khomeini.
A farkon watan Mayu, cibiyar tunawa da Imam Khomeini (RA) ta gayyaci kungiyoyin 'yan kasar Iran domin halartar taron tunawa da wafatin na Imam Khomeini.
A cikin wani jawabi, kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ta ruwaito, cibiyar ta bukaci mutane, hukumomi, kungiyoyi, jam'iyyun siyasa, masana, manazarta, shehunnan malamai, 'yan wasa da duka mutane daga kowanne bangare na rayuwa da su halarci tarurruka kan al'amarin wanda ke da sosa zuciya.
Ta ma bayyana cewa sakamakon samun saukin annobar Coronavirus, cibiyar ta shirya sosai domin yin tarurrukan da kyau a duka fadin kasar a wannan shekarar.
Post a Comment