Header Ads

Manjo Janar mai ritaya ya yi kira ga Isra'ila da ta shirya yaki da Hezbollah

Tsohon shugaban majalisar tsaron Isra'ila, Manjo Janar mai ritaya Yaacov Amidror, ya yi kira ga Isra'ila da ta shirya yaki da Hezbollah.

"Ya kamata mu kasance a shirye domin matsawa daga kowanne bangare tare da karfi iri daya." Kamar yadda Amidror, wanda ya ke tsohon mai bada shawara kan tsaro ne ga Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya nemi da a yi.

"A yayin da muke ware rundunar sojoji masu yawa domin su yi aiki a yamma da gabar kogin Jordan, za mu fuskanci kalubale sosai a yaki da Lebanon domin zai kasance mai sarkakiya saboda zai bukaci kayayyaki masu yawa da kuma kudi." Ya kara da cewa.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta Teghrib News Agency ta ruwaito, a watan da ga gabata, Amidror ya fadawa kafar watsa labaru ta Maariv cewa yana sa ran sojojin Isra'ila su fara yaki da Hezbollah inda ya yi kira ga sojojin da su kara shiryawa.

Manjo Janar din mai ritaya ya yi kira wajen kara kaimi kan shirye-shiryen yaki da Iran, inda ya bayyana cewa, "Ba zai kasance mai sauki ba kan Iran da Hezbollah." 

Kalaman Amidror na zuwa ne sati daya bayan kungiyar Hezbollah ta yi atisayen sojoji kusa da kan iyakar arewacin Isra'ila.

No comments

Powered by Blogger.