Header Ads

Imam Khomeini ya samar da "ruhin 'yan uwantaka" domin taimakon ƙasashen da ake zalunta - Malamin ƙasar Lebanon

Sheikh Ali al-Khatib

Mataimakin shugaban majalisar koli ta Shi'a a Lebanon, Sheikh Ali al-Khatib, ya yi yabo ga wanda ya jagoranci juyin juya-halin musulunci wajen samar da ruhin 'yan uwantaka domin taimakon kasashen da suke a karkashin zalunci.

Sheikh Ali al-Khatib ya bayyana haka ne wajen taron da aka yi a babban birnin kasar ta Lebanon, Beirut, domin tunawa da rasuwar jagoran juyin-juya halin musulunci, Imam Khomeini, karo na 34.

"Muna godiya ga Jamhuriyar Musulunci, wadda ta tsaya tare da Lebanon tun a da da kuma lokacin mamayar Isra'ila." Kamar yadda Khatib ya bayyana.

"Jamhuriyar Musulunci ta kan yi murna tare da Lebanon yayin da ta yi nasara a kan abokan gaban ta, wannan kuwa saboda 'yan uwantaka ne, wadda Imam Khomeini ya samar a cikin Jamhuriyar Musulunci domin taimakon kasashen da ake zalunta." 

Da ya ke bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci har yanzu tana nan tare da abubuwan da jagoranta ya tsara, Khatib ya bayyana cewa Iran "Na tare da masu fafutika tana goyon bayan abubuwan da suka shafi duniyar Larabawa da kuma duniyar Musulunci a Falasdinu, Siriya, Lebanon da Iraki." 

Ayatollah Ruhullah Mosavi Khomeini ya rasu ne a shekarar 1989 yayin da ya ke da shekaru 86, kusan shekaru goma bayan nasarar juyin-juya halin musulunci, wanda ya haifar da hambarar da gwamnatin da ke samun goyon bayan Amurka ta Pahlavi wanda aka fi sani da Shah.

Imam Khomeini ya bar Iran tare da zama a Iraki, Turkiyya da Faransa na shekaru da dama inda daga nan ne ya samar da tafiyar daga tushenta wadda ta yi sanadiyyar hambarar da Shah tare da kafa Jamhuriyar Musulunci.

Ya samar da Jamhuriyar Musulunci ne bayan gudanar da zaben jin ra'ayi a shekarar 1979 inda kashi 98 na 'yan kasar Iran wadanda suka isa zabe suka amsa da "E" domin kafa Jamhuriyar Musulunci.

Shekaru talatin bayan rasuwarsa, har yanzu ana tunawa da Imam Khomeini a matsayin mutumin da ya canza alkiblar tarihi a Iran, tare da mayar da hankali a kan 'yanci da dogaro da kai.

No comments

Powered by Blogger.