Mutumin da ya kona Kur’ani a Sweden ya ce yana shirin sake kona shi cikin kwanaki 10
Mutumin da ya kona shafukan Kur’ani a wajen wani masallacin birnin Stockholm, wanda ya haifar da zanga-zanga da kuma tofin Allah tsine, ya shaida wa kafafen yada labaran Sweden jiya Alhamis cewa, ya yi niyyar kona wani Kur’anin a cikin kwanaki 10.
Bayan da ‘yan sandan Sweden suka ba shi izinin gudanar da bijirewar, Salwan Momika, mai shekaru 37, ya taka littafin addinin Musulunci mai tsarki tare da sanya wa shafukansa da dama wuta a gaban babban masallacin babban birnin kasar a ranar Laraba.
Kona Kur'anin mai tsarki da ya zo daidai da fara Sallar Idin layya da kuma karshen aikin hajjin shekara-shekara a Makka a kasar Saudiyya, ya haifar da fusata a ko'ina a Gabas ta Tsakiya.
Da yake magana da jaridar Expressen, Momika ya ce, ya san matakin da ya dauka zai haifar da martini, kuma ya samu "dubban barazanar kisa."
Duk da haka, yana shirin ƙarin ayyukan bijirewar a cikin makonni masu zuwa, in ji shi.
"A cikin kwanaki 10 zan kona tutar Iraki da Al-Kur'ani a gaban ofishin jakadancin Iraki a Stockholm," in ji shi.
’Yan sandan Sweden sun ba shi izini bisa kariyar fadin albarkacin baki, amma daga baya sun ce sun bude bincike kan “haifar da hargitsi a kan wata kabila,” tare da nuna cewa ya yi kone-konen a kusa da masallacin.
Momika, duk da haka, ya musanta cewa abin da ya aikata ya kasance "laifi na ƙiyayya" ko "tashin hankali ga kowace ƙungiya."
“’Yan sanda na da ‘yancin gudanar da bincike kan ko konawar laifin kiyayya ce. Suna iya yin daidai kuma za su iya yin kuskure,” Momika ya shaida wa jaridar, inda ya kara da cewa, kotu ce za ta yanke hukunci a karshe.
Izinin 'yan sanda na nuna bijirewar ya zo ne makonni biyu bayan da wata kotun daukaka kara ta Sweden ta yi watsi da matakin da 'yan sandan suka dauka na hana ba da izinin gudanar da bijirewar guda biyu a Stockholm wanda ya hada da kona Kur'ani.
‘Yan sanda a wancan lokaci sun bayar da misali da matsalar tsaro, bayan kona littafin Musulman da aka yi a wajen ofishin jakadancin Turkiyya a watan Janairu wanda ya kai ga zanga-zangar makwanni da dama, da neman a kaurace wa kayayyakin Sweden, da kuma kara dakile yunkurin Sweden na zama mamba a kungiyar tsaro ta NATO – wanda Ankara ke hana ta shiga.
Sai dai kotun daukaka kara a tsakiyar watan Yuni ta yanke hukuncin cewa ‘yan sanda sun yi kuskure wajen dakatar da wadannan gangamin bijirewar, tana mai cewa matsalolin tsaro da ‘yan sandan suka bayar bai isa a hana aukuwar bijirewar ba.
Post a Comment