Header Ads

Saudi Arabiya, Iraki, Jordan, Kuwait, Iran, Moroko da Kungiyar Musulmai ta Duniya sun bi sahun yin Allah wadai da kona Al-Qur'ani a Sweden

Masu zanga-zanga sun rike kwafin Al-Qur'ani yayin da suke zanga-zanga a gaban ofishin kasar Sweden da ke Istanbul a ranar 23 ga watan Janairun 2023 bayan da wani mai tsatstsauran ra'ayi, Rasmus Paludan, ya kona kwafin Al-Qur'ani a kusa da ofishin jakadancin Turkiyya a Stockholm.


Musulmai a fadin duniya sun bi sahun Saudi Arabiya da Turkiyya wajen yin Allah wadai da kona Al-Qur'ani da wani dan kasar Iraki ya yi a kusa da babban masallacin Stockholm a ranar Laraba. 

Yayin da wurin da al'amarin ya faru ke cike da 'yan sanda, Salwan Momika, dan shekara 37, wanda ya gudu zuwa Sweden shekaru da dama da suka wuce, a ranar Laraba ya taka Al-Qur'ani kafin daga bisani ya sawa shafukansa da dama wuta a gaban babban masallacin birnin kasar Sweden.

'Yan sanda sun ba shi damar yin zanga-zangar a matsayin kariya ga fadin albarkacin baki, sai dai daga baya sun bayyana cewa sun fara gudanar da bincike a cikin kona Al-Qur'anin da aka yi wanda ya fusata duniyar Musulmai.

Wannan ba shi ne na farko ba da wannan irin al'amari ke faruwa a Sweden.

A cikin watan Janairu, wani dan kasar Denmark a Sweden mai tsatstsauran ra'ayi ya kona kwafin Al-Qur'ani a kusa da ofishin jakadancin kasar Turkiyya da ke Stockholm, wanda shi ma ya fusata duniyar Musulmai.

Firaministan kasar Sweden, Ulf Kristersson, ya bayyana cewa zanga-zangar Momika "kan ka'ida ta ke amma wadda ba ta dace ba" kuma 'yan sandan ne za su kyale hakan ko a'a.

Al'amarin na zuwa ne a yayin da Musulmai a fadin duniya ke bukukuwan Eid Al-Adha.

Gwamnatin kasar Iraki a cikin wani jawabi da ta fitar da yammacin ranar Laraba ta yi Allah wadai "da cigaba da kona Al-Qur'ani da mutane masu tsatstsauran ra'ayi kuma masu matsalar kwakwalwa ke yi." 

"Wannan na yin nuni ne da kiyayya da kuma ruhin zalunci da ya keta ka'idojin 'yancin fadin albarkacin baki." Kamar yadda ta bayyana.

"Ba wai kawai masu nuna wariya bane amma suna ma ruruta rikici da kiyayya." 

"Wadannan abubuwa na shashanci, wadanda sun ci karo da dabi'un girmama banbance-banbance a tsakanin jama'a da imanin wasu, kai tsaye an yi Allah wadai da su." 

Kasar Jordan ta kira Ambasadan Sweden a Amman a ranar Alhamis, ta kuma ce al'amarin "neman tunzurawa ne da nuna wariya."

Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen ta ce wannan al'amari ne "na kiyayya mai hadari kuma yana nuni ne da kiyayya da Musulunci" da ke neman haifar da rikici.

Jawabin Ma'aikatar ya bayyana cewa kona Al-Qur'ani "ba za a taba" daukar sa a matsayin wani bangare na fadin albarkacin baki ba, inda ta kara da cewa "akwai bukatar a daina dabi'u da abubuwa na shashanci."

Ma'aikatar ta bayyana cewa kalaman batanci da dabi'u dole a dakatar da su kuma dole a habaka al'adar zaman lafiya da amincewa da juna.

Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Kuwait ta bayyana cewa kona Al-Qur'ani ya batawa Musulmai da ke fadin duniya rai, inda ta bayyana cewa mutane ya kamata su habaka dabi'un iya zama da juna.

"Wannan al'amari mai girma ya bata ran Musulmai da ke fadin duniya." Kamar yadda Ma'aikatar ta bayyana a cikin wani jawabi.

"Kasar Kuwait na tunawa mutanen duniya da duka kasashen duniya wadanda abin ya shafa abinda ya kamata su yi na daukar mataki a kan kiyayya da tsatstsauran ra'ayin addini, da kuma na dakatar da ayyukan kiyayya kan abubuwa masu tsarki na Musulmai." 

Kasar Iran ta shiga cikin sahun masu yin Allah wadai din a ranar Alhamis, inda ta bayyana al'amarin da "na tonon fada, wanda ba a sa hankali a cikin sa ba kuma wanda ba za a amincemawa ba." 

"Gwamnati da mutanen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba su amincewa da irin wannan cin mutuncin kuma da kakkausar murya sun yi Allah wadai da shi." Kamar yadda kakakin ma'aikatar kasashen wajen, Nasser Kanani, ya bayyana. 

"Ana zaton gwamnatin Sweden ta yi la'akari da mutuntaka da kuma yin adalci a kan wannan al'amarin, a yayin da kuma a bangare daya ta ke hana sake maimaita cin mutuncin abubuwa masu tsarki." Kamar yadda ya kara da cewa.

Kasar Moroko ita ma ta yi Allah wadai da kona Al-Qur'ani tare da kiran Ambasadan ta a Stockholm da ya dawo gida a ranar Laraba.

"Wannan sabuwar cutarwa da shashancin bai damu da ya Musulmai sama da biliyan za su ji ba, a wannan lokaci mai tsarki na aikin Hajji a Makkah da kuma biki mai albarka na Eid Al-Adha." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

"A dalilin wannan tonon fada akai-akai, a kan idon gwamnatin Sweden ba tare da ta yi wani abu ba" Moroko ta kirawo babban mai diflomasiyya a ofishin jakadancin Sweden kuma ta dawo da Ambasadan ta gida, kamar yadda ta kara da cewa.

A cikin watan Janairu, wani dan kasar Sweden da ke Denmark mai tsatstsauran ra'ayi ya kona kwafin Al-Qur'ani a kusa da ofishin jakadancin Turkiyya, wanda wannan ya haifar da zanga-zanga a duniyar Musulmai.

Kuma babban sakataren Kungiyar Musulmai ta Duniya (Muslim World League) kuma shugaban kungiyar malamai Musulmai, Mohammed bin Abdulkarim Al-Issa, ya yi Allah wadai da al'amarin wanda ya ce an yi shi ne a karkashin kulawar 'yan sanda.

Ya bayyana cewa a yayin da ya faru ne "a karkashin ikirarin aikata 'yancin fadin albarkacin baki," a hakikanin gaskiya, ya cutar, "a cikin abubuwa da dama, hakikanin abinda 'yanci ke nufi, wanda ke nema da a girmama kuma kada a tunzura wasu ta kowacce fuska."

Issa ya bayyana cewa irin wannan al'amari yana ruruta kiyayya ne, ya tunzura san kai na addini kuma bukatun tsatstsauran ra'ayi kawai zai yi wa aiki. Ministan Harkokin Kasashen Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, shima ya yi Allah wadai da zanga-zangar ta Momika, inda ya bayyana ta da abin kyama.

"Wani abu ne wanda ba za a amincemawa ba a kyale wadannan al'amurra da ke batanci ga Musulunci da sunan 'yancin fadin albarkacin baki." Kamar yadda ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.