Header Ads

Malamin majami'a a Afirka ta Kudu da ya musulunta bayan wasu "mafarkai akai-akai," ya yi aikin Hajji na farko a rayuwarsa

Ibrahim Richmond yayin da ya ke gudanar da aikin Hajji a Makkah, Saudi Arabiya, a ranar 27 ga watan Yuni, 2023.

Ibrahim Richmond, wanda ya ke malamin majami'a ne daga kasar Afirka ta Kudu wanda ya zama musulmi bayan mafarkai da ya rinka yi akai-akai kuma ya jagoranci dubban mabiyansa shiga addinin, ya gabatar da aikin hajji na farko a kasar Saudi Arabiya. 

"Zan bi tafarkin ... (Annabi Muhammad), kuma na yi imani ... miliyoyin mutane na 'yan Afirka ta Kudu za su bi wannan tafarkin domin ganin haske." Kamar yadda ya bayyana a cikin wani bidiyo da cibiyar sadarwa ta gwamnatin Saudi Arabiya ta dora a shafin ta na Titter. 

"Wannan shine tsaunin haske. Ni ne na farko a cikin iyalina da ya taba nan, wannan kasar, wannan kasar mai albarka." Kamar yadda ya bayyana.

Ibrahim ya kasance malamin kirista ne a da na tsawon shekaru 15 kuma shugaban wata coci a kasar Afirka ta Kudu, inda ya ke da kusan mabiya 100,000.

Ya bayyana cewa rayuwa ta canza masa ne bayan ya yi wasu mafarkai masu kama da juna akai-akai inda wata murya ke fada masa: "Ka fadawa mutanen ka su sanya fararen riguna." Inda daga baya ya gano cewa fararen rigunan na nufin "Takiya" ne, wata farar hula da Musulmai ke sanyawa yayin sallah.

Daga farko bai mayar da hankali gare shi ba inda ya ce "kawai mafarki ne," domin umarnin ya shafi Musulmai ne kawai kuma ba ya da wani amfani ga Kiristoci. "Sai ya sake dawowa, ya sake dawowa, a lokacin karshe sai muryar ta fusata ta ce, " A yanzu ka fadawa mutanen ka." 

Richmond ya karbi addinin Musulunci ne watanni uku da suka gabata, ya kuma canza sunansa zuwa Ibrahim. Dubban Kiristoci daga cocinsa su ma sun bi sahu, sun musulunta, kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

A cikin wani bidiyo aka dinga watsawa, a yanar gizo a watan Maci, Ibrahim da dubban mabiyansa an ga suna kalmar shahada.

"Abinda na ke cewa, su ma suna cewa. Wadannan dubban muryoyi na fadin daya ... me ma'anar kalmar Shahada za ta zama. Muna cikin farin ciki, sai kuma na ga 'yan uwa musulmai na zuwa. Sai na ce dama ina jiranku, dama ina jiranku, na yi mafarki za ku zo nan." Ibrahim ya bayyana yana kuka.

Ya ce Allah Ya sa ya yi aikin Hajji cikin sauki kuma cikin albarka. "Ina cikin farin ciki kuma na samu sa'a da aka bani wannan dama."

A cikin wani bidiyo wanda shafin Haramain ya wallafa a ranar Litinin, ya nuno shi lokacin da ya zo Makkah tare da fara gabatar da ibadoji na farko.

Hukumomin Saudi Arabiya sun bayyana aikin Hajji na bana a matsayin "wanda ya fi girma" a cikin shekaru domin kuwa mutane sama da miliyan biyu daga kasashen sama da 160 suka gudanar da aikin Hajjin wanda ake yi a duk shekara. 

Aikin Hajjin na zuwa ne a yayin da hukumomin Saudi Arabiya suka dakatar da bukatar cewa sai mace na da muharrami a cikin shekarar 2021.

A wannan shekarar, an dakatar da iyakance shekarun wadanda za su yi aikin na Hajji, hakan kuwa na nufin dubban tsofaffi za su kasance cikin masu gudanar da aikin Hajjin. 

Aikin Hajji dai daya ne daga cikin ginshikan addinin Musulunci wanda musulmai wadanda Allah Ya ba iko ya ke wajibi su yi, akalla sau daya a rayuwarsu.

No comments

Powered by Blogger.