Rashin girmama Al-kur'ani laifi ne a Rasha - Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, ya bayyana cewa rashin girmama Al-Qur'ani laifi ne a cikin tsarin laifuffuka da hukuncin su (panel code) da kuma tsarin mulki a kasar Rasha.
Vladimir Putin ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara a birnin Derbent da ke Jamhuriyar Dagestan da ke da 'yancin kan ta a cikin Tarayyar Rasha.
Yayin da ya ziyarci masallaci mai tarihi na Derbent, Putin ya hadu da wakilan Musulmai daga Dagestan, kamar yadda kafar watsa labarai ta Morning Express ta ruwaito.
Yayin da ya ke taya Musulmai murnar bukukuwan Eid Al-Adha, sai aka mika Al-Qur'ani ga Putin, inda ya yi godiya da wannan kyauta kuma ya bayyana cewa, "Al-Qur'ani abu ne mai tsarki ga Musulmai kuma ya kamata ya kasance mai tsarki ga saura. Laifi ne a cikin tsarin laifuffuka da hukuncinsu da kuma tsarin mulki. A kodayaushe za mu bi wadannan dokoki." Kamar yadda ya bayyana.
Post a Comment