Header Ads

Turkiyya ta yi Allah wadai da kona Al-kur'ani a ranar Idi a Sweden

 Ministan Harkokin Kasashen Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, na jawabi lokacin da ya karbi matsayin Minista a ranar 5 ga watan Yuni, 2023.

Ministan Harkokin Kasashen Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya yi Allah wadai da kona shafukan Al-Qur'ani da dama a kasar Sweden a ranar Laraba, inda ya bayyana hakan da "abu mara kyau" kuma "abin kyama" kamar yadda kafar watsa labarai ta AlARABIYA NEWS ta ruwaito.

Wani mutum ne ya yi zanga-zanga a kusa da babban masallacin Stockholm bayan 'yan sanda sun bayar da damar yin zanga-zangar, inda ta zo lokaci daya da bukukuwan Eid Al-Adha na Musulmai.

"Na tsinewa abin kyama da aka aikatawa Littafinmu mai Tsarki, Al-Qur'ani mai Tsarki, a ranar farko ta Eid Al-Adha." Kamar yadda Ministan Harkokin Kasashen Wajen na Turkiyya, Hakan Fidan, ya bayyana a kafar Twitter.

"Abu ne wanda ba za a amince da shi ba a kyale irin wadannan munanan abubuwa a kan Musulunci da sunan fadin albarkacin baki.

"Yin ko in kula da wadannan abubuwa kamar kasancewa cikin masu aikatawa ne." Kamar yadda ya kara da cewa.

Salwan Momika dan shekaru 37, wanda ya gudu daga Iraki zuwa Sweden shekaru da dama da suka wuce, ya nemi amincewar 'yan sanda domin ya kona littafi mai tsarki na Musulmai "Domin bayyana ra'ayi na dangane da Al-Qur'ani."

Kafin a gudanar da zanga-zangar, Momika ya ma shaidawa kafar watsa labarai ta TT news agency cewa yana so ya nuna amfanin fadin albarkacin baki.

Momika ya tattake Al-Qur'ani, ya sa siraran naman alade a kai kafin ya wurgar ya haure shi yayin da ya ke kada tutar kasar Sweden kamar yadda kafar watsa labarai ta ALARABIYA NEWS ta ruwaito.

Amincewar 'yan sanda a gudanar da zanga-zangar ya zo sati biyu ne bayan wata kotun daukaka kara ta yi watsi da matakin 'yan sandan na hana yin wasu zanga-zangar guda biyu da suka hada da kona Al-Qur'ani.

A lokacin 'yan sandan sun bayyana cewa akwai yiwuwar hakan ya haifar da matsalar tsaro.

Kona littafi mai tsarki na musulmai a kusa da ofishin jakadancin Turkiyya a cikin watan Janairu ya haifar da zanga-zanga ta makonni, an yi kira da a kauracewa kayayyakin kasar Sweden kuma a hana bukatar Sweden na shiga cikin kungiyar NATO.

Wasu al'amurran masu kama da haka sun haifar da manya-manyan zanga-zanga da fusata a baki daya duniyar Musulmai.

Ankara ta ga laifin 'yan sanda musamman da suka amince da a gudanar da zanga-zangar ta cikin watan Janairu.

Turkiyya ta hana bukata kasar Sweden na shiga kungiyar NATO saboda abinda ta ke kallo da kasawar Stockholm wajen murkushe Kurdawa wadanda ta ke kallo da " 'yan ta'adda."

No comments

Powered by Blogger.