Talauci a fadin Ingila ya jefa 'yan Birtaniya miliyan 11.3 cikin yunwa - Rahoto
Wani babban bincike da aka gudanar ya nuna yadda tsananin rashin abinci ya kai a fadin Birtaniya yayin da mutane a fadin kasar baki daya ke fama da hauhawar farashi da kuma talauci mafi girma a cikin mutane na da, da kuma na yanzu.
Sama da mutane miliyan sha daya ko kuma mutum daya a cikin bakwai a mutane a baki daya Ingila sun fuskanci yunwa a shekarar da ta gabata saboda karancin kudi, kamar yadda wani bincike daga wata kungiya da ke bayar da sadaka ta Trussell Trust ta bayyana.
Kamar yadda kungiyar ta bayyana, bayanan baya-bayan nan da aka samu kadan kenan daga cikin matsalolin kudin, inda matsalolin kudin ba wai kawai yunwa ya haifar a cikin 'yan Birtaniya ba.
Binciken ya nuna cewa abubuwan da talaucin ya haifar sun hada da kebewa daga cikin mutane, kadaici, basussuka da kuma shafar lafiya ta fili da ta kwakwalwa.
Trussell Trust ta bayyana cewa wuraren ajiye abincin ta sun rarraba abincin gaggawa kusan miliyan 3 a cikin watanni 12 da suka gabata, yayin da bukatar ta ma fi haka yayin annobar korona, yayin da mutane da dama suka samu kansu cikin yanayin da ba za su iya biyan kudin abinci ba da na samar da dumi ga dakuna ko gini.
Masu binciken sun gano cewa rashin isasshen kudin shiga shi ke sa mutane suke yanke alakoki, domin haduwa da abokai ko iyalai na cin kudi sosai.
Kamar yadda wani bincike a Ingila kafin wannan ya nuna, iya zama da yunwa ya zama al'ada a tsakanin 'yan Birtaniya da ke fuskantar hauhawar farashin abinci da ba a taba yi ba a baya da kuma wahalhalun talauci.
Gwamnatin Ingila ta bayyana cewa masu gidaje suna fuskantar karancin wadata a cikin shekaru biyu mafi girma tun shekarar 1950.
A yanzu haka, wannan matsala da ba a san karshen ta ba ta cigaba a karkashin mulkin jam'iyyar 'yan ra'ayin rikau (Conservative Party).
Masu sukar gwamnati sun dora laifi a kan 'yan ra'ayin rikau sakamakon wahalhalun rashin kudin shiga da mutane a mataki daban-daban ke fuskanta a cikin al'umma, kokarin tseratar da rayuwa a cikin tattalin arziki mai fuskantar kalubale, hakan ya sa 'yan Birtaniya da dama suka koma samun abinci daga ma'ajiyar abinci a yayin da ake tsaka da fuskantar wahalhalu da hauhawar farashi.
Alkawarin Firaminista Rishi Sunak na rage rabin hauhawar farashi baki daya a shekarar 2023 kafin zaben 2024 ya samu matsala sakamakon hauhawar farashin abinci, wanda ya haifar da takura ga kasafin kudin masu gidaje da tuni ya ke fuskantar matsala sakamakon haraji mai yawa da kuma kudin hayar gida.
Kamar yadda kididdigar baya-bayan nan ta nuna, hauhawar farashin abinci da abin sha ya kai kashi 18.3 cikin 100 a cikin watan Mayu, kuma 14.6 a cikin 100 a watan Yuni.
Hauhawar farashin abinci a ya haifar da babbar matsala ga yanayin jin dadin rayuwa a baki daya fadin Birtaniya tun da aka fara kididdigar haka a shekarar 1950 kamar yadda rahoton wanda kafar watsa labarai ta Press TV ta wallafa ya nuna.
Post a Comment