Header Ads

Amurka za ta sake aika makamai na dala miliyan 500 zuwa Ukraine


Amurka ta shirya kai wasu makamai ta jirgin ruwa na miliyoyin daloli zuwa Ukraine.

Wannan shine karo na arba'in da daya da Amurka ta tura taimakon soji ta jirgin ruwa ga Kiev tun bayan da Moscow ta kaddamar da aikin soji na musamman a Donbas a cikin watan Fabrairun 2022.

"A yau, gwamnatin Biden da Harris na ayyana sabon taimakon tsaro ga Ukraine, a yayin da muke cigaba da kasancewa tare da mutanen kasar Ukraine." Kamar yadda mataimakiyar babban sakataren kula da 'yan jaridu na fadar White House, Olivia Dalton, ta bayyana a ranar Talata.

Gwamnatin Amurka ta ayyana shirin ta na kai taimakon soji da ya kai dalar Amurka miliyan 500 ga Ukraine.

Sabon taimakon da za a kai ta jirgin ruwa an ruwaito zai hada da motocin yaki 50 (motocin Bradley da Stryker) da kuma makamai masu linzami kala daban-daban, makaman harba roka na HIMAS da kuma makaman tsaron sararin samaniya na Patriot.

Niyyar taimakon na Amurka shine karfafa sojojin kasar Ukraine wajen kai manyan hare-hare daga wuraren tsaron ta, wanda ta fara yi a farkon watan nan, sai dai ya kasa cimma wani cigaba a fagen yaki.

Tun farkon yakin Ukraine, kafofin watsa labaran Amurka akai-akai suna yin rahotannin makamai da Amurka ke kaiwa ta jirgin ruwa domin karfafa fadan sojojin Kiev, inda su ma wasu kasashen kungiyar NATO suka kai taimakon soji na biliyoyi.

Zuwa watan Janairu, Amurka da kawayenta sun kai taimako na kananan makamai sama da miliyan 100, sama da gidajen harsashin manyan bindiga miliyan 100 da kuma harsasan tankuna sama da 100,000 ga kasar Ukraine.

A yanzu haka, shugaban tsare-tsare na Pentagon ya bayyana cewa taimakon soji da Amurka ke kaiwa kasar Ukraine a yakin da ta ke yi da Rasha ya sa kamfanonin kera makamai na Amurka cikin takura. 

"Kokarin taimakawa Ukraine ya haifar da takura" a kan kamfunan kera makamai na kasa, kamar yadda Colin Kahl, sakatere mai aiki kuma mai karamin matsayi ga tsare-tsaren tsaro, ya bayyana a wajen wani taro na matasan kungiyar NATO a farkon watan Yuni. 

Sai dai, saboda rashin kakkautawa wajen kai makamai kasar Ukraine, kasar Sin ta dora alhakin cigaba da yaki da Rasha kan kasashen yamma kamar yadda kafar watsa labarai ta Press TV ta ruwaito.

"Idan dagaske muna so mu tsayar da yaki, mu tseratar da rayuka, mu samu zaman lafiya, ya kamata mu daina kai makamai filin yaki." Kamar yadda jami'i na musamman na kasar Sin kan harkokin da suka shafi kasashen Turai da Asia, Li Hui, ya shaidawa manema labaru a Beijing a ranar 2 ga watan Yuni.

Kasar Rasha ita ma tana kallon yin ambaliyar makamai daga kasashen yamma zuwa Ukraine a matsayin yunkurin da ba zai cimma nasara ba na kokarin canza sakamakon yakin. Moscow ta bayyana cewa kai makamai Kiev zai kara kawai ne a kan mace-mace da asarori.

No comments

Powered by Blogger.