Putin ya yi gargadi ga NATO da cewa Rasha ta kai makaman nukiliya Belarus
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin, a ranar Juma'a ya bayyana cewa kai tactical nuclear weapons (makaman nukiliya wadanda aka tsara domin amfani da su a filin yaki) kasar Belarus, wanda wannan ne karon farko da ya tabbatar da an yi hakan, tunatarwa ce ga kasashen yamma cewa ba za su iya cin galaba a kan Rasha ba.
Yayin da ya ke magana a wajen taron tattalin arziki a St Petersburg, ya bayyana cewa tuni aka kai makaman nukiliyar kasar Belarus, amma ya bayyana cewa bai ga dalilin da zai sa Rasha ta yi amfani da makaman nukiliya a yanzu ba.
"Kamar yadda kuka sani, muna tattaunawa da abokiyarmu (shugaban kasar Belarus (Alexander) Lukashenko, cewa za mu kai wani bangaren makaman nulikya da ake iya amfani da su a filin yaki zuwa kasar Belarus - hakan ya faru." Kamar yadda ya bayyana.
"Makaman nukiliyar na farko an kai su kasar Belarus. Amma na farkon kawai, na kashin farko. Amma za mu yi wannan aikin baki dayansa zuwa karshen bazara ko kuma karshen wannan shekarar." Cewar Putin.
Cewa Moscow ta kai wadannan makaman - makaman nukiliya da ke cin gajeren zango wadanda za a iya amfani da su a filin yaki - a wajen kasar Rasha tun bayan rushewar Tarayyar Sobiya na da niyyar yin gargadi ne ga kasashen yamma kan kai makamai da goyon bayan kasar Ukraine, kamar yadda shugaban na Rasha ya bayyana.
"Karara wannan gargadi ne saboda duk wadanda ke tunanin za su iya cin galaba a kan mu kada su manta da yadda yanayin ya ke." Cewar Putin.
Lukashenko, wanda babban abokin Putin ne, a ranar Talata ya bayyana cewa sun fara karbar makaman nukiliyar na Rasha da suka hada da wasu da ke da karfin da ya lunka har sau uku kan makaman atomic bomb da Amurka ta harba a kasar Japan a shekarar 1945.
Shugaban na Rasha ya bayyana dama a watan Maci cewa ya amince ya kai makaman nukiliyar kasar Belarus , inda ya bayyana cewa dama Amurka na kai irin wadannan makaman a kasashen turai da dama a cikin shekarun da suka gabata.
Amurka ta yi suka dangane da matakin na Putin, amma ta bayyana cewa ba za ta canza matsayarta a kan makaman nukiliyar wadanda ake iya amfani da su a filin yaki ba kuma ba ta ga alamun Rasha na shirin amfani da su makaman nukiliya ba.
Duk da haka, Washington da kawayenta da kasar Sin suna kallaon duk wani al'amari a tsanake a wannan matakin na Rasha, kasar Sin ta sha yin gargadi kan amfani da makaman nukilya a yakin Ukraine.
Post a Comment