Shekaru tara bayan babbar fatawar Ayatollah Sistani a kan 'yan ta'addan Daesh a Iraki
A ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2014, 'yan ta'addan Daesh sun yi kisan kiyashi inda suka kashe akalla daluban sojan sama da mafi yawan su 'yan Shi'a ne sama da 1,700 a harabar makarantar Tikrit Air Academy, wadda aka fi sani a da da Camp Speicher, a arewacin Iraki a abinda aka bayyana da mafi munin ta'addanci da kungiyar ta'addancin ta yi.
Bayan labari ya wastu cewa Tikrit ta fada hannun Daesh, manyan dalibai sun nemi kananan daluban da su sa kayan fararen hula su bar sansanin da al'amarin ya afku, su koma gida domin yin hutun kwanaki 15 domin su tsira.
Sai dai a kan hanyarsu kamar yadda shaidu suka bayyana, 'yan ta'addan da kuma sauran yaruka da ke dauke da makamai a tare da su sai suka kama su.
'Yan ta'addan sun rarraba su daban-daban, 'yan Sunni, Shi'a da wadanda ba musulmai ba inda suka kaisu wurare daban-daban tare da kashe su a wani irin mummunan yanayi, kamar yadda shaidu suka bayyana.
Wasu daga cikin gawarwakin an yi masu kabarin bai daya wasu kuma aka jefa su cikin Rafin Tigirs.
Kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na kafar watsa labarai ta Press TV, kwana daya bayan wannan mummunan al'amari a ranar 13 ga watan Yunin 2014, babban malamin addini a kasar Iraki, Ayatollah Ali Sistani, ya yi wani kira wanda ya zamanto sananne cewa mutanen kasar Iraqi su dauki makamai domin tunkarar kungiyar 'yan ta'addan ta Daesh.
Fatawar ta zo ne a yayin da 'yan ta'addan na Daesh ke kara matsawa zuwa babban birnin kasar Baghdad bayan sun kwace garuruwa masu muhimmanci da ke arewacin kasar Iraki na Jalulah da Saaiydiyah.
Fatawar ta kasance wani babban al'amari a cikin tarihin siyasa na wannan zamanin a yankin kuma wani canji wajen fada da 'yan ta'addan na kasa-da-kasa.
Fatawar, wadda ta yi kira ga duk wani dan kasar Iraqi mai lafiya ya dauki makami domin tunkarar barazanar Daesh, ta samu babbar amsa inda dubunnan mutane suka taru kan Daesh.
A shekarar ta 2014, kamar yadda ya ke a cikin rahoton, 'yan ta'addan sun kama birane da dama a kasar Iraki wadanda suka hada da Samarwa, Mosul da Tikrit bayan sauran yankuna, hakan kuwa ya sa gwamnatin kasar Iraki ta kasa yin iko da kan iyakarta da Jordan da kuma Siriya.
A lokacin, kasar Iraki na fama da rigingimu akai-akai a tsakanin bangarorin siyasa da dama, kuma hukumar sojin Iraki na fama da matsaloli da suka hada da yaduwar rashawa, rashin shugabanci da kuma sojoji wadanda ba su biyayya.
Wannan kutse tsararre yayin da kasar ke fama da matsalolin siyasa na cikin gida ya haifar da rushewar sojojin Iraki da Amurka ta yiwa horo da kuma 'yan sandan kasar a kashi uku na fadin kasar.
Kwana daya bayan wannan kisan kiyashi, Ayatollah Ali Sistani, wanda ke samun matukar girmamawa a baki daya al'ummar Iraki, ya yi jawabi ga kasar wadda ke cikin makoki.
A yayin sallar Juma'a a gari mai tsarki na Karbala, aka bayyana fatawar a maimakonsa wadda ke kira ga duka 'yan kasar Iraki su kare kasar, mutanen ta, mutuncin 'yan kasarta da kuma wurarenta masu tsarki.
"'Yan kasa wadanda za su iya daukar makamai domin su yi fada da 'yan ta'adda, su kare kasarsu da mutanenta da wuraren ta masu tsarki, su sadaukar su shiga cikin jami'an tsaro domin cimma wannan manufa mai tsarki." Kamar yadda wakilin Ayatollah Sistani ya bayyana a yayin sallar Juma'a a birni mai tsarki na Karbala.
"Wanda ya sadaukar domin kare kasarsa, da iyalinsa da mutuncinsa zai kasance shahidi." Kamar yadda ya kara da bayyanawa.
Kiran na wajibi domin tashi tsaye domin fada da 'yan ta'addan na kowa da kowa ne, ba wai na mabiya wani addini ko kungiya ba. Kira ne domin kasar Iraki.
Wannan kira na Ayatollah Sistani, wanda aka watsa a kafar talabijin din kasar ta Iraki, ya haifar da babban tasiri domin kuwa ya hada kan 'yan kasar Iraki domin tunkarar makiyinsu baki daya. A sakamakon haka, aka kirkiro "Popular Mobilization Units (PMU)" wadda aka ma sani da Al-hashd al-Shabi a ranar 15 ga watan Yuni.
Wadda tun asali ta kunshi bangarorin Shi'a daban-daban ne bakwai, nan-da-nan bangarorin Sunni, Kiristoci da Yazidi suka shiga PMU wadda a da tana aiki ne ita kadai.
Mutane da yawa masu shekaru daban-daban sun nemi shiga wadannan kungiyoyi, kusan miliyan uku. Sababbin kungiyoyin sai suke fuskantar matsalar makamai, wanda hakan ya ragu ne da taimakon Iran.
Taimakon Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga PMU da kuma shugabancin babban kwamandan yaki da ta'addanci, Laftanar Janar Qassem Soleimani, wanda ke samun taimako daga sanannen kwamandan kasar Iraki mai yaki da ta'addanci, Abu Mahdi Al-Muhandis, ya tabbatar da samun nasara a kan Daesh.
A ranar 9 ga watan Disambar 2017, tsohon Firaministan kasar Iraki, Haider al Abadi, ya bayyana cin nasara a kan Daesh.
Rawar da fatawar Ayatollah Sistani ta taka wajen wannan fadan babba ce wanda hakan ya haifar da samun nasara a kan Daesh a kasar Iraki.
Post a Comment