Header Ads

Ƙungiyar Haɗin kan Musulmai ta yi Allah wadai da kisan ƙaramin yaro Bafalasdine da Isra'ila ta yi tare da kira da a gudanar da bincike

Muhammad Haytham Tamimi


Kungiyar Hadin kan Musulmai (OIC) ta yi Allah wadai da kisan karamin yaro bafalasdine da gwamnatin Isra'ila ta yi a yankin da aka mamaye na yamma da gabar kogin Jordan.

Kungiyar ta ma nemi a gudanar da bincike mai zaman kansa na kasa-da-kasa a cikin laifin.

Kamar yadda kafar watsa labaru ta Tasnim News Agency ta ruwaito, sojojin Isra'ila sun harbi yaron mai shekaru biyu da rabi, Muhammad Haytham Tamimi, ne a kai a ranar Alhamis a kauyen Nabi Salah da ke kusa da Ramallah, yayin da shi da kuma mahaifinsa, Haytam Tamimi, ke cikin motarsu da ke kofar gidansu.

Muhammad ya samu manyan raunuka a kai yayin da mahaifinsa ya samu raunuka a kirji. An tafi da karamin yaron wani asibiti mai suna Sheba Hospital, inda ya kasance a nan ana kula da shi kafin a bayyana rasuwarsa a safiyar ranar Litinin.

A cikin wani jawabi bayan harbin, hukumar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa sojojin ta sun yi kuskure ne kan karamin yaron bafalasdine da mahaifinsa da tunanin wasu mayakan Falasdinawa.

OIC "ta yi Allah wadai da laifuffukan da sojojin mamayar Isra'ila ke cigaba da aikatawa, na baya-bayan kuwa shine laifin da ya yi sanadiyyar rasuwar karamin yaro bafalasdine dan shekara biyu da rabi, Muhammad Al-Tamimi, wanda aka harba a kai." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin kungiyar ta kasa-da-kasa mai mambobin 57 a ranar Talata.

Kungiyar da ke Jeddah ta bayyana cewa, ta "dauki wannan laifin a matsayin daya daga cikin jerin laifuffuka da Isra'ila ke yi ga mutanen Falasdinawa, ciki har da yara, inda yaran da ba su gasa 28 ba suka yi shahada a hannun mai mamaya Isra'ila tun farkon wannan shekarar." 

OIC ta ma yi kira "da a samar da bincike mai zaman kansa na kasa-da-kasa a cikin wannan laifin." 

Sojojin Isra'ila na yin kutse a birane da dama da ke yamma da gabar kogin Jordan da aka mamaye da sunan tsare abinda ta kira Falasdinawa "da ake nema." A mafiyawancin lokuta kutsen kan gamu da turjiya daga mazauna yankunan.

Majalisar dinkin duniya ta bayyana shekarar 2022 a matsayin shekarar da ta fi muni ga Falasdinawan da ke yamma da kogin Jordan a cikin shekaru 16. Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa akalla 171 a yamma da gabar kogin Jordan da kuma gabashin al-Quds da aka mamaye a shekarar da ta gabata, ciki har da sama da yara 30. Akalla wasu 9,000 suka raunata. 

Kamar yadda wani rahoto na shafin watsa labaru da ke Ingila, Middle East Eye, ya nuna, sojojin Isra'ila da yahudawa yan-kama-wuri-zauna sun kashe Falasdinawa akalla 119 a yamma da gabar kogin Jordan da gabashin Jerusalem al-Quds tun watan Janairu da kuma wasu 34 a zirin Gaza. 

Baki daya dai, yara 28 sojojin Isra'ila suka harba tun farkon shekarar nan, ciki akwai bakwai a zirin Gaza, kamar yadda kafar watsa labarun Falasdinawa ta musamman, Wafa news agency, ta bayyana a cikin wani rahoto a ranar Litinin.

No comments

Powered by Blogger.