Header Ads

Yahaya Bello ya tsira da ransa bayan wasu 'yan daba suka bude wuta kan kwamban motocinsa

Gwamna Yahaya Bello na Kogi

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a ranar Asabar ya bayyana cewa wasu 'yan daba sun kai hari kan ayarin motocinsa yayin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa Lokoja.

Gwamnan na kan hanyarsa ta zuwa Lokoja ne daga Abuja yayin da harin ya afku a kauyen Banda da ke wajen babban birnin jihar.

A cikin wani jawabi a ranar Asabar, kwamishinan sadarwa, Kingsley Femi Fanwo, ya bayyana cewa an tare ayarin gwamnan ne tare da kai masu hari daga wasu mutane wadanda aka yi imanin cewa magoya bayan Alh Muritala Yakubu Ajaka ne da misalin karfe 12:30 na rana a ranar Asabar.

"An yi harin ne kusa da sansanin sojojin ruwa, kilomitoci kadan daga Lokoja inda ayarin motocin Muritala Yakubu Ajaka suke, bayan sun ga na gwamnan, suka rufe hanyar kuma wasu daga cikin 'yan dabar sa da ke dauke da makami suka fara harbin kan-mai-uwa-da-wabi a kan ayarin gwamnan.

"Kuma wata mota Tundra mai alamar SDP da tutar SDP ta hana motar gwamnan wucewa kuma motar Tundra din mai dauke da alamar SDP na dauke da wasu mutane wadanda ke rike da manya da kananan bindigogi. Gwamnan ya bar wurin da al'amarin ya afku ba tare da wani rauni ba kuma kada a tsorata domin gwamnan na cikin koshin lafiya.

"Wasu jami'an tsaro da wasu jami'ai da ke tare da gwamnan sun samu raunuka kuma an yi gaggawar kai su asibiti domin kula da lafiyarsu. 

"Muna neman mutanen jihar Kogi da su kwantar da hankalinsu domin jami'an tsaro na kula da dukkan al'amurra domin tabbatar da cewa an kama 'yan dabar da ke da alhakin kai harin. Gwamnatin jihar za ta tabbatar da cewa ana bin doka da oda domin wadanda suka kai harin sai sun fuskanci hukunci.

"Gwamnan ya yi gargadin cewa kada wani dan jam'iyyar APC ya kai harin ramuwar gayya saboda rashin tsaro daga kowanne bangare zai fuskanci hukunci mai tsauri." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin.

No comments

Powered by Blogger.