Header Ads

An gudanar da bukin Eid al-Ghadeer a haramin Imam Ali da ke Najaf

An kawata titunan da suke kaiwa zuwa haramin Imam Ali (AS) da ke Najaf a kasar Iraki saboda Eid al-Ghadeer.

Mutane daga Iran, Iraki bayan na sauran wurare sun zo haramin Imam Ali (AS) da ke Najaf, wanda shine Imami na farko a duniyar Shi'a.

Kamar yadda Iran Press ta bayyana a cikin wani rahoto, kubbar haramin da hanyoyin shigarsa an kawata su da tutoci koraye, hanyoyin kuma da wadanda suka kawo ziyara suke bi aka kawata su da furanni.

Shugaban Kungiyar dabbaka addinin Musulunci, Hojjatoleslam Mohammad Komi, ya bayyanawa kafar watsa labarai ta Iran Press cewa saboda muhimmancin da Manzon Allah (S) ya sa a kan Eid al-Ghadeer, al'amarin yana da matukar muhimmanci a tsakanin Musulmai.

Ya bayyana cewa Eid al-Ghadeer ana daukar sa da matukar muhimmanci a cikin al'ummar Iran saboda al'amarin "Wilaya" wanda shine Annabi Muhammad (S) ya gabatar da Imam Ali (AS) a matsayin magajinsa da ya kasance kalifansa kuma Imam (shugaba) na Musulmai, Amir ul-Mumeneen.

No comments

Powered by Blogger.