Matashi, 30, ya rataye kansa watanni hudu bayan aurensa a jihar Jigawa
Wani mutum mai shekaru 30, Usman Sanigoga, da ke zaune a Akula Quarters da ke karamar hukumar Babura a jihar Jigawa ya rataye kansa.
Kakakin hukumar tsaron farin kaya ta Nijeriya (NSCDC) a jihar Jigawa, Malam Adamu Shehu, ya bayyana haka a Dutse a ranar Alhamis.
Ya bayyana cewa matar Sanigoga ta same shi a rataye a cikin dakin da suke kwana a ranar Laraba bayan ta dawo daga wata ziyara da ta kai.
Ya ma kara da cewa matar Sanigoga, wanda daukar hoto ya ke yi, ta bayyana cewa ya ajiye ta a wani gidan 'yan uwansu da misalin karfe 2 na rana tare da alkawarin zai dawo ya dauke ta zuwa gida da yamma.
Bayan ta yi jira na tsawon lokaci bai dawo ba, ta kira layin wayarsa sosai amma ba a daga ba, sai ta yanke shawarar ta hau wani mashin din wanda za ta biya kudi domin ta koma gida.
Ta kara da cewa ta tarar da gidan a kulle, sai ta nemi taimakon mai mashin din da ya tsallaka ta katanga ya bude babbar hanyar shigar.
"Bayan an bude kofar sai ta ga mashin din mijinta an ajiye shi a yanayin da ba haka aka saba ba. Sai ta hanzarta ciki inda ta tarar da gawarsa a rataye daga rufin silin din dakin kwanansu.
"Ganin haka sai ta fita daga hayyacinta ba tare da sanin inda ta ke ba sai mai mashin din ne ya nemi taimako kafin makwafta su hanzarta zuwa wurin da al'amarin yan faru." Kamar yadda ta shaidawa hukumar NSCDC.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Channels Television ta ruwaito, an garzaya da gawar zuwa asibiti, inda a can ne likita ya tabbatar da cewa Sanigoga ya rasu.
Wani bincike da NSCDC ta gudanar ya nuna cewa wata durowa da ke gefen gadon su ce aka yi amfani da ita a saman wani gado mai fadi domin kaiwa ga rufin silin din inda aka makala igiya a jikin wani karfe.
Shehu ya bayyana cewa makusantan Sanigoga sun fadawa NSCDC cewa yana da matsalar kwakwalwa da kan iya sake tashi.
Ma'auratan dai sun yi aure ne kimanin watanni hudu da suka gabata kuma suna zaune cikin farin ciki a tare kafin faruwar al'amarin, kamar yadda makwafta suka bayyana.
Hukumar ta NSCDC na kan cigaba da bincike cikin al'amarin yayin da shi kuma marigayin aka jana'izar sa kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Post a Comment