Akidar Imam Khomeini a siyasa ta duk masu son adalci ce - Sheikh Zakzaky
Akidar siyasa ta Imam Khomeini, jagoran juyin-juya halin musulunci, ba ta tsaya kan musulmai ba kawai amma ta "baki daya 'yan Adam ce" kamar yadda jagoran harkar musulunci a Nijeriya ya bayyana.
A cikin wata tattaunawa da ya yi da shafin yanar gizo na kafar watsa labarun Press TV wanda ya danganci tunawa da wafatin jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran karo na 34, Sheikh Ibraheem Zakzaky ya yi jinjina da yabo cikin girmamawa ga marigayin.
"Na kan ce Imam Khomeini na nan a raye kuma mutane su yi koyi da akidarsa." Kamar yadda jagoran harkar musuluncin ya bayyana wanda kuma daya ne daga cikin almajiran marigayin wanda ya ke jagora kuma shugaban Juyin-juya halin Musulunci.
Sheikh Zakzaky na da almajirai masu yawa kuma musulmai na girmamashi a fadin Afirka, musamman musulmai a Nijeriya, saboda akidunsa da ke kokarin kawo canji a siyasance da dagewarsa a kan gaskiya da adalci, kamar yadda kafar ta Press TV ta bayyana.
Malamin dan Nijeriya da matarsa sun fuskanci azabtarwa daga hukumomin Nijeriya na shekaru masu yawa, inda baki dayansu ke fama da rashin lafiyar da ke shafar rayuwa kuma an hana su fita waje domin neman kulawar likitoci.
Tun cikin watan Disambar shekarar 2015, lokacin da sojojin Nijeriya suka azabtar da shi ba tare da sassautawa ba kuma aka kona gidansa, ya kasance a tsare ba bisa ka'ida ba kusan shekaru biyar.
Sanannen shehin malamin kan yi magana a kan Juyin-juya halin Musulunci wanda Imam Khomeini ya jagoranta da yadda ya samu kwarin gwiwa daga gwagwarmayar Imam Khomeini kan masu girman kai da fasadi na lokacin.
"Akidarsa ba wai ta tsaya kan musulmai ba ne kawai, amma ta duka 'yan Adam ce. Ko menene ka yi imani da shi, kowa na son adalci." Kamar yadda ya shaidawa kafar watsa labaru ta Press TV.
Sheikh Zakzaky, wanda shine shugaban harkar musulunci a Nijeriya da ba ta amfani da tashin hankali wajen gwagwarmayar ta da ma'abota girman kai na cikin gida da waje, ya ce akidar Imam Khomeini ta kara masa karfin gwiwa.
"Wannan ce akidar Imam Khomeini. Ta kowa ce. Muna tare da duk wadanda ake zalunta, a duk inda suke." Ya tabbatar, inda ya ke nufin irin akidar siyasa ta Imam Khomeini.
Shehin malamin da ke Nijeriya a tsawon shekaru na da almajirai masu yawa a Nijeriya da sauran kasashen Afirka saboda jarumtarsa wajen kare hakkin bil-adama, fadin gaskiya da sauransu.
Post a Comment