Gwamnonin Nijeriya sun goyi bayan Tinubu kan cire tallafin mai
Gwamnonin Nijeriya sun goyi bayan matakin shugaban kasa, Bola Tinubu, na kawo karshen biyan tallafin mai a kasa.
Kamar yadda kafar watsa labaru ta Channels Television ta ruwaito, gwamnonin wadanda suka yi magana yayin ziyarar da suka kai fadar shugaban kasa sun bayyana jin dadin su da matakin da shugaban kasar ya dauka na cire tallafin, shugabanci wanda ke tafiya tare da kowa da kuma kwarewarsa a kan al'amurran da suka shafi kasa.
Karkashin jagorancin shugaban su gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, kungiyar ta gwamnonin Nijeriya (NGF) ta yabawa Tinubu kan samar da mafita kan babban al'amarin tallafin man, inda suka yi alkawarin yin aiki tare da shi domin saukake matsalar karamin lokaci na matakin.
"NGF za ta yi yadda ta saba yi a tsarin mulki na yin aiki cikin hadin kai da kai." Kamar yadda AbdulRazaq ya fada a wani bangare na jawabin.
Gwamnonin sun ma yi bayani dangane da wahalhalun al'ummun jihohinsu, inda suka tabbatarwa shugaban kasar goyon bayansu wajen samar da mafita ta hanyar majalisar tattalin arzikin kasa (NEC).
A cikin jawabansa, Tinubu ya nemi gwamnonin da kada su mayar da hankali sosai kan banbance-banbancen da ke tsakaninsu, amma su mayar da hankali ne wajen warware matsaloli da wahalhalun mutane.
Tinubu ya bayyana cewa ya kamata ne a kalli kasar a matsayin wani babban iyali, inda ya kara da cewa kyakkyawan shugabanci shi ne zai kare makomar damakaradiyya.
"Za mu iya ganin alamun rashin wadata a fuskokinmu mutanenmu. Rashin wadata ba gado ba ne, daga al'umma ne. Matsayarmu itace mu kawar da rashin wadata. Mu ajiye bangarancin siyasa mara tushe a gefe, muna a nan ne domin mu tattauna a kan Nijeriya da kuma gina kasa.
"Mu iyali ne da ke zaune a gida daya muna barci a dakuna daban-daban, idan mun kalli al'amarin a haka muka kara kaimi, za mu fitar da al'ummarmu daga rashin wadata. Zuciyar da ke da niyya wani fili ne na samar da sakamako.
"A yanzu haka a cikin dakin nan muna da banbance-banbancen al'ada da siyasa, amma mu kasa daya ne. Hadin kai da daidaituwar kasar nan ya dogara a kan mu.
"Muna a damakaradiyya ne kuma ya kamata mu kula da damakaradiyyar. Tsari ne da ke da wahala ba mai sauki ba. Idan wani na tunanin yana da sauki, kalli sauran kasashen da suka yi sama da shekara dari a damakaradiyya." Kamar yadda Tinubu ya bayyana.
Post a Comment