Header Ads

Hukumar yaƙi da rashawa ta jihar Kano ta gayyaci Ganduje kan bidiyoyin dala

Tsohon gwamnan jihar Kano, Ganduje

Hukumar sauraron kararrakin jama'a da yaki da rashawa ta jihar Kano (PCACC) ta gayyaci Abdullahi Ganduje kan bidiyoyin dala.

A cikin shekarar 2017 ne dai kafar watsa labarai ta Daily Nigerian, wadda ke watsa labaran ta a yanar gizo, ta saki wasu bidiyoyi na Ganduje da ke yin ikirarin yana karbar biyan samun hadin kai daga wasu 'yan kwangila.

A cikin bidiyoyin, an nuna Ganduje na karbar daloli kafin daga bisani ya sa a cikin babbar rigarsa fara. 

Tsohon gwamnan ya yi watsi da ikirarin, inda ya bayyana cewa bidiyoyin an shirya su ne.

Sai dai a yayin da ya ke jawabi yayin tattaunawa ta kwana daya a ranar Laraba kan "Yaki da rashawa a jihar Kano," shugaban hukumar ta PCACC, Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya bayyana cewa an tabbatar da gaskiyar bidiyoyin, kamar yadda PM News ta ruwaito.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa tun da aka saki bidiyoyin mutane ke ta kalubalantar sa da ya tabbatar da rashin laifi ko akasin haka na tsohon gwamnan a kan al'amarin.

Ya bayyana cewa hukumarsa ta kaddamar da bincike a cikin shekarar 2018 amma ta kasa cigaba saboda a lokacin Ganduje, wanda gwamna ne a lokacin, yana da kariyar mulki (immunity).

Yayin da ya ke jawabi a cikin wani shiri a ranar Alhamis, Rimingado ya tabbatar da cewa an gayyaci Ganduje domin tambayoyi.

No comments

Powered by Blogger.