Kona Alkur'ani: Mun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da wadanda suka aikata shi - Ofishin Sayyid Zakzaky
A cikin wani jawabi da ofishin jagoran harkar Musulunci a Nijeriya, Sayyid Ibraheem Zakzaky, ya fitar a ranar 1 ga watan Yuli na shekarar 2023, ofishin shehin malamin ya yi Allah wadai da kona Alkur'ani da aka yi a kasar Sweden da wadanda suka kona Alkur'anin tare da kira da a gaggauta hukunta su.
Ofishin ya bayyana cin zarafin Al-Kur'ani da aka yi a kasar Sweden a matsayin abinda ya raunata zukatan dukkanin musulmi da masu neman 'yanci a duniya, tare da cewa ya zama wajibi ga duk wani mai 'yanci da kada ya yi shiru a kan wannan aiki.
Ofishin ya bayyana cewa tabbas kona Al-Kur'ani ba wai cin fuska ne kawai ga Musulunci da musulmi ba, cin fuska ne ma ga dukkanin addinan duniya da mabiyansu.
"Wannan labari mara dadi na cin zarafin Alkur'ani mai girma a kasar Sweden ya raunata zukatan dukkanin musulmi da masu neman 'yanci na duniya.
"Tabbas, kona Alkur'ani mai tsarki ba wai cin fuska ne ga Musulunci da musulmi ba, cin fuska ne ma ga dukkanin addinan duniya da mabiyansu. Don haka ya zama wajibi ga duk wani mai 'yanci da ka da ya yi shiru a kan wannan aiki.
"Mun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki da wadanda suka aikata shi kuma muna kira da a gaggauta hukunta su." Kamar yadda ya ke a cikin jawabin da aka wallafa a kafar sada zumunta ta Facebook.
Wani mutum ne dai mai suna Salwan Momika, mai shekaru 37 wanda ya gudu zuwa Sweden shekaru da dama da suka wuce, a ranar Larabar da ta gabata ya taka Alkur'ani kafin daga bisani ya sawa shafukansa da dama wuta a gaban babban masallacin birnin kasar ta Sweden.
Wannan kuwa ba shi ne karo na farko ba da wannan irin al'amari ke faruwa a Sweden.
A cikin watan Janairu, wani dan kasar Denmark a Sweden mai tsatstsauran ra'ayi ya kona kwafin Alkur'ani a kusa da ofishin jakadancin kasar Turkiyya da ke Stockholm, wanda hakan ya fusata duniyar musulmi.
Kasashe da dama dai sun yi Allah wadai da wannan mummunan aiki na kona Alkur'ani da aka yi a ranar Laraba wadanda suka hada Saudi Arabiya, Iraki, Jordan, Kuwait, Iran da Moroko.
Post a Comment