Header Ads

Kungiyar Houthi da ke Yemen ta haramta shigo da kayayyakin Sweden sakamakon kona Alkur'ani


Kungiyar Houthi da ke kasar Yemen ta haramta shigo da kayayyakin kasar Sweden arewacin kasar, wanda ke a karkashin ikonta, domin nuna rashin amincewar ta da kona Alkur'ani da aka yi a Sweden yayin wata zanga-zanga.

Ministan kasuwanci na Houthi, Mohammed al-Mutahar, ya bayyana cewa haramtawar "sako ne na kin amincewa" da al'amarin, wanda ya bayyana da "aiki na kaba'ira" kamar yadda ya ke a cikin wani rahoto na PM News.

Ministan kasuwancin ya bayyana cewa haramtawar a yankin da Houthi ke da ikon "kayyadajje ne" saboda kayayyakin da Sweden ke shigowa da su Yemen ba su da yawa.

Kasashen Musulmai da dama sun yi Allah wadai da kona Alkur'ani wanda wani dan gudun hijira daga Iraki ya yi a yayin zanga-zanga a Stockholm cikin watan da ya gabata.

Duk da cewa 'yan sandan Stockholm daga farko sun amince da kona littafin na Alkur'ani da aka yi, gwamnatin Sweden daga baya ta yi Allah wadai da al'amarin inda ta bayyana shi da aiki na "kiyayya da Musulunci."

Mayakan Houthi da ke Yemen dai sun kama iko da yankuna da dama na arewacin kasar ne a karshen shekarar 2014, wanda hakan ya haifar da yakin basasa, wannan kuwa ya tilastawa gwamnatin Yemen ficewa daga babban birnin kasar, Sana'a. Tun tuni dai gwamnatin ta koma birnin da ke da tashar jirgin ruwa da ke kudanci na Aden.

No comments

Powered by Blogger.