Header Ads

NSCIA ta yi kira ga hukumomin Sweden da su hana kona Alkur'ani

Shugaban NSCIA, Sultan na Sokoto, Muhammadu Sa'ad Abubakar

Majalisar Harkokin Addinin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA) ta yi kira ga hukumomin kasar Sweden da su dauki matakan da suka dace domin hana cigaba da keta alfarmar Alkur'ani a kasar.

Majalisar na magana ne a kan kona Alkur'ani da aka yi a gaban babban masallacin Stockholm da wasu makiya musulunci suka yi a kwanakin baya.

Majalisar a cikin wani jawabi daga mataimakin babban Sakataren ta, Farfesa Salisu Shehu, ta ce ba wani Littafi mai Tsarki da ya kamata a keta alfarmar sa da nuna masa rashin girmamawa kamar yadda ake yi a Sweden.

Majalisar ta yi imanin cewa Sweden ba za ta amince a kona tutar kasar ta ko Bibul a irin wannan yanayi ba.

"Majalisar na yin kira ga hukumomin Sweden a matsayin wani abu na gaggawa da ta yi bincike a cikin al'amarin, ta bayyana rahotonsa ga kowa, kuma ba wai kawai ta tabbatar da an yi adalci ba amma a gani cewa an yi adalcin." 

Majalisar ta NSCIA ta ce ta hadu da sauran musulmai da sauran shugabannin kwarai da mutane a fadin duniya wajen yin Allah wadai, da babbar murya, da wannan aiki na tonan fada da babbar kaba'ira na kona Alkur'ani mai girma, kamar yadda kafar watsa labarai ta PM News ta ruwaito. 

"Wannan kaba'ira kuma mummunan aiki a fili ya ke yana yin nuni ne da hauhawar kiyayya da Musulunci tare kuma da kariya ga masu kiyayya da Musulunci wadanda kiyayyar su ga Musulunci da Musulmai ba ta san iyaka ba.

"Ayyuka da abubuwan da wadannan masu kiyayya da Musuluncin ke fadi babban rashin nuna ko in kula ne da kuma rashin girmamawa ga me Musulmai kusan biliyan biyu da ke fadin duniya za su ji."

Majalisar ta NSCIA ta kuma yi kira ga Musulmai da ke fadin duniya da su kwantar da hankulansu su kuma kasance masu zaman lafiya da bin doka kan wannan tonan fadan.

Gwamnatin Sweden a cikin wani jawabi ta ofishin Harkokin Kasashen Wajen ta ta yi Allah wadai da al'amarin.

"Muna Allah wadai da wadannan al'amurra, wadanda ba sa yin nuni ta kowacce fuska da ra'ayin gwamnatin Sweden." Kamar yadda ta bayyana.

No comments

Powered by Blogger.