Header Ads

Yadda aka sa tutar Eid al-Ghadeer a Windsor City Hall da ke Canada


A ranar 18 ga watan Dhul al-Hijja na shekarar 1444 bayan hijira, wadda ta yi daidai da 7 ga watan Yuli na shekarar 2023, gidauniyar Imam Hussain Charitable Foundation ta daga tutar Eid al-Ghadeer a Windsor City Hall da ke Windsor, jihar Ontario a kasar Canada.

A cikin wani bidiyo wanda gidauniyar ta Imam Hussain Charitable Foundation ta sa a shafin ta na kafar sada zumunta ta Facebook, an ga yadda mutane da dama suka taru domin sa tutar.

Sadik Pirani, daya daga cikin wadanda suke a gidauniyar ta Hussain, ya bayyana cewa, "Ba za mu iya bayyana farin cikin da muke ciki ba domin ganin wannan tuta na filfilawa a City Hall a yau, kuma muna cikin farin ciki da kasancewar mu a birnin, saboda sun karbe mu." Kamar yadda ya bayyana a cikin bidiyon.

Da yammacin ranar, an haskaka ginin kuma da haske kore domin bukin ranar ta Eid al-Ghadeer, kamar yadda kafar watsa labarai ta The 14 News ta ruwaito.

Ginin Windsor City Hall dai shine cibiyar gwamnatin Windsor da ke jihar Ontario a kasar Canada. Ofishin magajin garin da kuma majalisar Windsor City Council suna a gini na musamman ne da ke 350 City Hall Square West inda kuma sauran wuraren ayyuka na birnin ke kusa da ginin 400 City Square East a cikin Windsor, kamar yadda shafin Wikipedia ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.