Header Ads

Yadda aka yi bukukuwan Eid al-Ghadeer a kasashen Iran, Yemen, Iraki, Pakistan da Turkiyya

Bukin Eid al-Ghadeer a kan titin Baliasr mai tsawon kilomita 10, wanda shi ne ya fi kowanne titi tsawo a Tehran, a ranar Litinin.
 
Mutane da dama a cikin kasahe sun yi bukukuwan Eid al-Ghadeer, wanda ke nuni da ranar da Manzon Allah (S) ya nada Imam Ali ibn Abi Talib (AS) a matsayin kalifansa kuma shugaban Musulmai na gaba. 

A kasar Iran, mutane da dama sun yi bukukuwan Eid al-Ghadeer a yankunan kasar daban-daban. Shugaban Juyin-juya Halin Musulunci a Iran, Ayatollah Seyed Ali Khamenei, ya yi yafiya ko kuma rage wa'adin wadanda aka samu da laifi har mutum 2272 sakamakon ranar ta Eid al-Ghadeer.

Shugaban sashen shari'a, Mohseni Ejei, ne ya tura sunayen masu laifin inda kuma shugaban ya amince da ya yi yafiya ko rage wa'adin da aka dibar masu kamar yadda tsarin mulki ya tanada, kamar yadda Mehr News Agency ta ruwaito.

A tare da Iran, Musulmai 'yan Shi'a a kasashen yankin daban-daban sun yi bukukuwan Eid al-Ghadeer, wanda ke yin nuni da ranar da Manzon Allah (S) ya nada Imam Ali ibn Abi Talib (AS) a matsayin kalifansa kuma shugaban Musulmai na gaba.

Musulmai a Yemen sun gabatar da zagayen gari mai cike da mutane a ranar Lahadi a babban birnin kasar Sana'a domin ranar ta Ghadeer.

'Yan kasar Iraki su ma sun shirya sosai domin gudanar bukin na Eid al-Ghadeer Kum. Shugabannin yarurrukan Iraki suna fata cewa babban al'amarin na Eid al-Ghadeer Kum ya kasance alami na hadin kai a tsakanin 'yan Shi'a da Sunni da sauran Musulman Iraki da na duniya. Harami daban-daban da ke Iraki a shisshirya su an kawata su domin bukin na Eid al-Ghadeer, kamar yadda kafar watsa labarai ta Mehr News Agency ta ruwaito.

Haramin Imam Ali (AS), Imami na farko na Shi'a, an kawata shi da furanni domin ranar Eid al-Ghadeer.

A Karbala, saboda ranar Eid al-Ghadeer, an kawata haramin Imam Hussein (AS) da na Hazrat Abbas (AS) an kawata su da furanni bayan alluna da aka kawata da aka jingina duk da sunan Imamim Shi'a na farko. A Kadhmayn da Samarra, haramin Imaman Shi'a biyu (Amincin Allah ya tabbata a garesu) an kawata su da furanni a ranar da ta ke sananna.

Kamar yadda kafofin watsa labarai na Iraki suka bayyana, gwamnonin Najaf, Karbala, Basra, Dhi Kar, Diwaniyeh, Maysan, Wasit, Diyala, Babil da Muthanna sun bayyana kulle ofishoshin gwamnati a hukumance a wadannan yankuna da suke a kudanci da tsakiyar Iraki a ranar Eid al-Ghadeer Kum.

Hakama a kasar Pakistan, mutane da dama sun taru a birnin Lahore, babban birnin jihar Punjab, inda wasu manyan mutane na Iran da sanannun 'yan siyasa da malaman addini na Pakistan suka halarta. Sanannen mawakin nan, Abouzar Ruhi, wanda ya yi wakar "Salam Farmandeh" da "Hello Commander" wadanda suka shahara a kasar Iran da sauran kasashen yankin shima ya halarci taron wanda aka yi a Lahore. Wadanda suka halarci taron sun nuna hadin kai da nuna kasancewa ana tare a tsakanin Musulmai maza da mata domin kare abubuwa na addinin Musulunci da kuma tunkarar shirin raba su.

Mutanen kasar Turkiyya kamar sauran Musulmai a duniya su ma sun yi bukin Eid al-Ghadeer, wanda ke nuni da ranar da Manzon Allah (S) ya nada Imam Ali ibn Abi Talib (AS) - Imamin Shi'a na farko a matsayin kalifansa kuma shugaban Musulmai na gaba.

Mutanen Turkiyya da ke yankin Hatay sun yi bukin Eid al-Ghadeer, kuma a yayin bukin, mutanen na Hatay sukan dafa abinci ne na musamman da ake kira "Hirisi" wanda ake yi ta hanyar hada naman da aka yi layya da alkama tare da dafawa a manya-manyan tukwane tare da rarraba abincin ga mutanen da suke makwaftansu, musamman iyalan da ba su da hali sosai.

Sun tafi wurare masu tsarki inda suka kunna turaren wuta a wuraren tare da yin addu'o'i, kamar yadda kafar watsa labarai ta Heber Turk ta ruwaito.

A ranar ta Eid al-Ghadeer, mutane da dama masu sayar da abubuwa da masu kula da shaguna ba su bude wuraren ayyukansu ba inda su ma suka shiga cikin bukukuwan.

Bayan nan, a Diyarbakir da ke gabashi, an yi bukin na Eid al-Ghadeer ne ta hanyar rarraba taimako "Ihsan,."

No comments

Powered by Blogger.