Header Ads

BAKI SHI KE YANKA WUYA: Ƙwararan dalilai 22 da suka sa DSS suka hana a ba El-rufai Minista

Tsohin Gwamnan Kaduna, El-rufai 

Mutane da dama sun yi mamakin ganin yadda sunan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya fito cikin mutane ukun da Majalisar Dattawa ta ƙi tantance su.

Sai dai yanzu wani binciken musamman da PREMIUM TIMES ta yi ya tabbatar da cewa Hukumar SSS ce ta fitar da rahoto a kan sa dangane da waɗansu aika-aika masu nasaba da take haƙƙin ɗan Adam da kuma tulin kwafen ƙorafe-ƙorafen da aka riƙa aikawa a kan sa.

Akwai zarge-zargen sa da riƙa yin wasu kalamai ba tare da ya tunanin daidai ko rashin dacewar yin kalaman ba, ballantana kuma tunanin abin da furucin na sa ka iya haifarwa ba.

Yayin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya aika da sunayen ministoci 48, Majalisar Dattawa ta mai da masa sunaye 45 da ta tantance, amma banda sunaye 3, waɗanda cikin su har da na El-Rufai, wanda ake kallo a matsayin makusanci na ƙut-da-ƙut ga Tinubu.

Tun a gaban Majalisa wurin tantancewa aka fara gantsara wa El-Rufai, amma aka yi rufa-rufa cewa ya rage wa Shugaba Tinubu ya ɗauki matakin da ya dace kan duk wani wanda ake da rahoton ƙorafe-ƙorafe a kan sa.

Baya ga El-Rufai, Majalisar Dattawa ta ƙi aika wa Tinubu da sunan Sani Ɗanladi daga Taraba da kuma Stella Okotete ɗaga Delta.

Bayan ta tuntuɓi majiyoyi da dama sahihai, PREMIUM TIMES ta fito a karon farko ta zayyana dalilan da suka hana a tantance El-Rufai.

Majiyoyin mu sun nemi a sakaya sunan su, saboda ba a ba su iznin yin magana da ‘yan jarida ba. Amma kuma sun ce akasarin dalilan da su ka sa aka ƙi tantance El-Rufai, duk jama’a sun san su, ba abin ɓoye ba ne.

Majiya ta ce SSS sun yi ƙorafi kan El-Rufai cewa a baya har zuwa kwanan nan, ya riƙa sakin baki ya na caɓa maganganu ba tare da yi wa bakin sa linzami ba. Kuma maganganun masu barazana a cikin al’umma.

Sai dai kuma majiyar mu ta ce SSS ba su tunkari El-Rufai da zarge-zargen da ake yi masa ba.

1. Rashin Yi Wa Bakin Sa Linzami:

Wannan zargi shi ne muhimmi daga cikin rahoton da SSS su ka yi kan El-Rufai.

Tsohon Gwamnan Kaduna ya yi ƙaurin suna wajen yin kasassaɓa da katoɓara a cikin jama’a. Irin waɗannan maganganu kuwa su ne suka zame masa ‘baki shi ke yanka wuya’ a yanzu.

Kaɗan daga cikin su akwai kakkausan kalaman da ya taɓa yi kan masu adawa ko rigima da shi, inda ya buga misali da tsaffin shugabannin Najeriya biyu – Marigayi Umaru ‘Yar’Adua da Goodluck Jonathan.

2. Kakkausan Kalaman El-Rufai A Kan ‘Yar-Adua da Goodluck Jonathan:
“‘Shugabanni Biyu Da Suka Ja Da Ni, Ɗaya Ya Sheƙa Barzahu, Ɗaya Kuma Ya Koma Otuake Da Zama”.

A nan El-Rufai bai ambaci sunayen su ba, amma kowa ya san da waɗanda ya ke, kuma kowa ya san ya yi takun-saƙa da su biyu ɗin.

A lokacin da ya yi wannan furucin a cikin jama’a a Kuduna, an riƙa mamaki, har wasu na ganin kamar mutumin ya na da albatsutsai.

3. Kalaman El-Rufai Kan Yadda Ya Ke Fifita Tsarin Muslim-Muslim A Muƙaman Takarar Gwamna Da Mataimaki A Kaduna:

Wannan kalami na sa ya sha suka sosai a faɗin ƙasar nan, har ana kallon cewa El-Rufai ya na ƙoƙarin ruruta rabuwar kai da rikicin ƙabilanci ko na addini.

SSS sun ce wannan furuci na El-Rufai ya ƙara faɗaɗa rashin yarda da nesanta amintaka tsakanin Musulmi da Kiristoci a ƙasar nan.

5. Zaɓen 2019: Barazanar El-Rufai Cewa Za A Maida Gawarwakin Masu Katsalandan Zuwa Ƙasashen Su A Cikin Makara:

El-Rufai ya yi furucin a lokacin da ya ke sake takarar gwamna a Kaduna karo na biyu. Ya yi kakkausan kalaman ne kan ƙungiyoyin sa-ido da wasu ƙasashen waje masu magana kan lamarin da ya shafi zaɓe a Najeriya.

Majiya ta ce SSS sun ce saboda wannan furuci da El-Rufai ya yi, yanzu haka an yana shi shiga ƙasar Amurka.

Sai dai kuma PREMIUM TIMES ba ta tabbatar shin an hana shi ɗin ko kuma Amurka ba ta yana shi ɗin ba.

6. Katoɓara Da Saɓon Da El-Rufai Ya Yi A Cikin 2013:

Majiya ta ce SSS ta bankaɗo wani rubutu da El-Rufai ya watsa a cikin 2013, wanda ta ce “saɓo ne ya yi a shafin sa na Tiwita.” Ta ce rubutun ya haifar da ruɗani a ƙasar nan sosai.

7. Zarge-zargen Danne Haƙƙin Ɗan Adam:

Waɗannan zarge-zarge sun haɗa har da kisan mabiyan jagoran Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zazzaky, a Zariya da Kaduna, cikin 2015.

Yayin da Gwamnatin El-Rufai ta tabbatar cewa ta sa an rufe gawarwaki sama da 300 a ɓoye, IMN ta yi iƙirarin cewa an kashe masu sama da mutum 1,000, kuma wasu ma da sauran ran su aka binne su.

Sojoji ne suka yi kisan, amma dai lamarin ya samu goyon bayan Gwamnatin El-Rufai.

Maimakon a tuhumi sojoji kan kisan da suka yi, sai Gwamnati ta kama El-Zazzaky ta tuhume shi da matar sa da laifin kashe wani soja ɗaya.

A ƙarshe dai kotu ta kori ƙarar, bayan El-Zazzaky da matar sa sun shafe shekaru a tsare. An kasa samun su da laifin kisan, sai aka sallami ƙarar cikin Yuli, 2021.

8. Gabatar Da Kisan ‘Yan Shi’a A Kotun ICC Ya Kawo Wa El-Rufai Cikas Wajen Tantance Shi:

Wannan ƙara da aka shigar a ICC, kotun Majalisar Ɗinkin Duniya, ta karta wa El-Rufai rubutun alamar-tambaya a goshin sa. Kuma har yanzu ICC na gudanar da bincike a kan kisan.

9. Zarge-zargen Kama Mutane Barkatai Ya Na Kullewa Da Sunan Adawa, Ƙwace Kadarori Da Rushe Gine-ginen ‘Yan Adawa:

10. Zargin Amfani Da Ƙarfin Gwamnati Ana Yi Wa Masu Zanga-zanga Rubdugun Da Kan Kai Ga Kisa:

11. Zargin Sayar Da Kadarorin Gwamnatin Tarayya:

12. Ƙararraki Da Ƙorafe-ƙorafen Almubazzaranci, ‘Yin Amfani Da Kore Da Iyalan Sa Wajen Yin Wata Harƙalla A Lokacin Ya Na Shugaban BPE Da Ministan FCT Abuja:

PREMIUM TIMES ta gano kotu ta kori irin wannan ƙarar da aka maka El-Rufai. Amma SSS sun ce yanzu haka akwai wata a Babbar Kotun Tarayya.

14. SSS Sun Ce An Fi Ƙorafi Kan El-Rufai Fiye Da Sauran Sunayen Ministoci 47:

Sun buga misali yadda aka riƙa ƙorafe-ƙorafe birjik a soshiyal midiya kan sa, sai kuma yadda wasu suka yi zanga-zanga a Majalisar Dattawa, lokacin tantancewa, suna nuna ba su so a tantance El-Rufai.

15. Ƙorafe-ƙorafe Kan El-Rufai A Kotun ECOWAS, ICC.

16. Ƙorafin Da Hukumar Kare Haƙƙin Musulunci, Islamic Human Rights Commission Ta Aika Wa Tinubu Kan El-Rufai:

17. Samun Tabbacin ICC Ta Ƙarɓi Ƙararrakin Da Aka Maka El-Rufai A Kan Zargin Kisan Kiyashi Da Cin Zarafin Ɗan Adam:

18. Ƙararrakin Da Aka Maka El-Rufai A Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan Adam Ta Ƙasa, ‘Amnesty International’, Dangane Da Kwace Filaye A Kaduna Bayan Kotu Ta Hana Shi Ƙwacewa:

19. Ƙorafe-ƙorafen Rashin Ganin Darajar Dattawan Arewa Da Ci Masu Fuska:

20. Kasassaɓar El-Rufai Da Ya Taɓa Cewa Tinubu Gogarman Ɗan Harƙalla Ne, Ba Zai Taɓa Zama Mataimakin Tinubu Ba:

19: Yunƙurin Zuga ‘Yan Majalisar Kaduna Su Soke Shari’ar Muslunci A Jihar Kaduna, Don Ya Samu Goyon Bayan Kiristoci:

Yayin da Kakakin Majalisar Kaduna na lokacin, Yusuf Zailani ne ya fito ya yi masa wannan zargin, wani ɗan majalisa na lokacin mai suna Yusuf Salihu, ya ƙaryata zargin.

20. El-Rufai: Ɗan Mage Ba Ka Ɗaɗin Goyo:

Majiya ta ce SSS ta zargi El-Rufai da yawan cin amanar shugabannin da suka raine shi a gwamnatance. Kamar yadda ya riƙa yi wa tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, wanda ya ɗauko shi ya fara haɗa shi da Obasanjo, sai kuma na baya-bayan nan, Shugaba Muhammadu Buhari.

21. Zulwajahaini: Zargin El-Rufai Ya Na Tufka Da Warwara:

Kwanan nan ya ce ko an ba shi muƙamin minista ba ya so, a bai wa wasu, ga yara nan masu tasowa. Amma ana ambatar sunan sa, sai ya fara shirye-shiryen tafiya tantancewa.

22. Yawan Fito Da Tsare-tsaren Da Ke Gallaza Wa Masu Ƙaramin Ƙarfi Da Lalata Dukiyar Jama’a A Jihar Kaduna.

Sun haɗa da ruguje kasuwa ba tare da biyan diyya ba, kora da rushe gidajen ‘low-cost’ masu sauƙin kuɗi, korar dubban ma’aikata da sauran su. Korar sarakunan gargajiya da sauran su.

Rahoton ya ce mutum maras tausayi kamar irin haka, bai dace a ba shi muƙamin aikin jama’a a ƙasa ba.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Muyiwa Adekeye, Mashawarcin El-Rufai Kan Yaɗa Labarai, amma bai ce komai ba.

No comments

Powered by Blogger.