Header Ads

Wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta yanke hulda da Isra'ila saboda yaƙin da take yi da Falasɗinu In ji 'yan'uwa musulmi mabiya Shaikh Zakzaky

Farfesa Abdullahi Danladi na Resource Forum a tsakiya yana jawabi ga manema labarai

Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Shaikh Zakzaky ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yanke hulda da Isra'ila, a daidai lokacin da ake ci gaba da yakin da Isra'ilar ta kaddamar kan Falasdinu.

Da yake zantawa da manema labarai a jiya Asabar a Abuja, Shugaban Dandalin Resource Forum na Harkar Musulunci, Farfesa Abdullahi Danladi, ya yi Allah-wadai da yadda ake ci gaba da ta’azzara yakin da danniya a yankunan Falasdinawa.

A cikin jawabin nasa, Farfesa Danladi ya ce, “Dalilin taronmu shi ne mu sake yin jawabi a gare ku da kuma al’ummar Nijeriya nagari kan ci gaba da ta’addancin da haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) ta Sahayoniya take yi wa al’ummar Palastinu.

 “A rubuce yake cewa Jagoranmu Shaikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky (H) yana fafutukar ganin an hada kai an nuna goyon baya ba kawai ga Palasdinawa ba, har ma da dukkan raunanan al’umma da ake zalunta a fadin duniya.

 “Abubuwan da suka faru na baya-bayan nan a Gabas ta Tsakiya, musamman ma kasar Palastinu da HKI ta mamaye sun bude wani babi a tarihin dan Adam. Sama da shekaru saba'in da biyar 'yan sahayoniya suna kashewa tare da korar Falasdinawa da karfi daga gidajensu karkashin kulawar munafukan Amurka da mugayen kawayenta. Ya zuwa yanzu dai an kashe dubbai da dama wadanda yawancinsu yara da mata ne. Asibitoci, makarantu, sansanonin 'yan gudun hijira da wuraren ibada ba su tsira daga laifukan yaki na Isra'ila ba.

"Ina waɗanda ake kira masu kare hakkin ɗan Adam da masu fafutukar kare martabar dimokradiyya da ɗan Adam? Ba wai kawai Amurka ta yi shiru bane, a'a a cikin mummunan cin zarafi ga rayukan bil'adama da kuma 'yanci, ba tare da kunya ba ta aika da jiragen ruwa na yaki don taimakawa tare da tallafa wa Isra'ila a ci gaba da kisan kiyashi da take yi kan fararen hula.

"Tallafin goyon bayan da aka nuna wa raunanan al'ummar Palastinu da ake zalunta a duniya baki daya daga mabiya addinai daban-daban da kuma kasashe daban-daban, gami da wasu yahudawa masu tunani na gaskiya, shaida ce karara kan cewa haramtacciyar kasar Isra'ila a yau ta fito a matsayin wacce aka fi kyama, kuma la'ananniya a duniya."

Ya ci gaba da cewa: Sanannen abu ne cewa Isra'ila ta ci gaba da karya yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da kuma kudurorin da suka shafi wannan haramtacciyar kasar da suke ci gaba da mamaye yankin Falasdinu mai karamin karfi. Don haka, tsayin daka da dakewar da ake gani daga ƙungiyar HAMAS daidai yake kan ka'idojin kare kai da kare hakki.

Waɗannan jajirtattun mutane sun tsaya tsayin daka a gwagwarmayarsu mai tsarki. Don haka muna jinjina da kuma tabbatar muku da addu'o'inmu da goyon bayanmu. Hakika Harkar Musulunci a karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) tun sama da shekaru talatin take ci gaba da nuna goyon bayanta ga Palastinu da ake zalunta.

"Za mu so mu yi kira ga wadanda suka jahilci tarihi da abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya, kuma suke kallon sahyoniyawan a matsayin 'yan'uwansu a cikin imani, su sake bude idanuwansu su kalli al'amuran ba ta gilashin ta'assubancin imani, launin fata, da dai sauransu ba. Hare-haren baya-bayan nan. a kan Coci da asibitoci sun isa su nuna cewa wannan al'amarin mummuna ya wuce batun addini, a'a laifi ne ga bil'adama, wanda dole ne a yi Allah wadai da shi.

 “Bacin rai da hare-haren wuce gona da iri ke nunawa yana bayyana raunin haramtacciyar kasar Isra’ila ne kawai, kuma alama ce ta rugujewarsu a nan gaba kadan. Nasara ta ƙarshe daga Allah za ta tabbata ga waɗanda aka zalunta.
 "A kan wannan batu, muna kira da kakkausar muryoyinmu ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta yanke duk wata alaka ta difulomasiyya da cinikayya da tsaro da wannan haramtacciyar kasa ta Sahayoniyawan Israila.”

No comments

Powered by Blogger.