Header Ads

Zaɓen gwamna: Mutum 2,318,919 za su yi zaɓe a Imo, 1,833,160 a Kogi, 1,017,613 a Bayelsa, inji INEC

Shugaban Hukumar zaɓen Nijeriya, Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta wallafa cikakken bayani kan katittikan masu zaɓe (PVC) da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba a matakin rumfunan zaɓe a zaɓuɓɓukan gwamna da za a yi a jihohin Bayelsa, Imo da Kogi a ranar Asabar ta makon gobe.

Hakan ya biyo bayan taron da hukumar ta yi a ranar Litinin domin sake nazarin shirye-shiryen da ta ke yi na zaɓuɓɓukan gwamna da za a yi a jihohin uku a ranar 11 ga Nuwamba, 2023.

A sanarwar da Babban Kwamishina kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai Da Ilmantar Da Masu Zaɓe a INEC, Mista Sam Olumekun, ya rattaba wa hannu, hukumar ta ce: “Kamar yadda aka yi a zaɓuɓɓukan baya-bayan nan, ciki har da Babban Zaɓen 2023, hukumar ta wallafa cikakken bayani kan katittikan masu zaɓe (PVC) da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba a jihohin uku a matakin rumfunan zaɓe.

“Haka kuma bayanin ya bada yadda aka rarraba rumfunan zaɓen a Yankunan Ƙananan Hukumomi, Cibiyoyin Rajista ko Mazaɓu, da sunayen rumfunan zaɓen, da alƙaluman lambobin su, da yawan masu zaɓe da su ka yi rajista, da kuma yawan katittikan masu zaɓe da aka karɓa da waɗanda ba a karɓa ba.

“Shi ma wani muhimmin abu shi ne, jadawalin ya ba da sunaye da inda rumfunan zaɓe guda biyu da ake da su a Jihar Bayelsa da 38 da ake da su a Imo waɗanda ba su da masu zaɓe da su ka yi rajista.

“Lissafin na jihohin uku ya nuna cewa daga cikin masu zaɓe 1,056,862 da su ka yi rajista a Jihar Bayelsa, mutum 1,017,613 sun karɓi katittikan su, sannan ba a karɓi 39, 249 ba. A Jihar Imo, masu zaɓe da su ka yi rajista su 2,419,922 ne, waɗanda daga cikin su mutum 2,318,919 sun karɓi katittikan su amma 101,003 ba su karɓa ba, yayin da a Jihar Kogi, daga cikin masu zaɓe 1,932,654 da su ka yi rajista, mutum 1,833,160 sun karɓi katittikan su, sannan 99,494 ba su karɓa ba."

Hukumar ta yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a lamarin zaɓuɓɓukan da su yi la'akari da cewa duk fa wata ƙuri'a da aka samu a rumfar zaɓe wadda ta haura yawan ƙuri'un da aka karɓa to shaida ce cewar an yi aringizo kenan. 

Ta ƙara da cewa za a yi amfani da yawan katittikan zaɓe da aka karɓa wajen lissafa tsarin wanda ke kan gaba.

No comments

Powered by Blogger.