Header Ads

Gwamnatin Tinubu ba za ta ƙaƙaba wa jama'a takunkumin hana magana ba - Minista

Alhaji Mohammed Idris (a hagu) a lokacin tattaunawar sa da gidan talbijin na Arise... A daren Asabar

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta shigo da dokokin hana 'yan jarida da sauran jama'ar Nijeriya faɗin albarkacin bakin su ba.

Sai dai kuma ya ce ya kamata mutane su sani cewa 'yancin faɗin albarkacin baki ya na tattare da haƙƙin sanin ya-kamata da ya rataya a wuyan kowa. 

Ministan ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya fito a karon farko aka tattauna da shi a shirin "Newsnight" na gidan talabijin na ARISE a Abuja a daren Asabar, inda amsa tambayoyi dangane da ƙudirorin wannan gwamnatin kan harkar yaɗa labarai da shirin wayar da kan al'umma da kuma burukan 'yan Nijeriya.

Idris ya bayyana cewa ya shafe makwanni takwas da su ka gabata ya a nazari kan ayyukan ita kan ta Ma'aikatar Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai ta Tarayya, tare da tattaunawa da Sassa da Hukumomin ma'aikatar.

Ya ce: "Mun san abin da mu ke so ta zama, amma tilas ne mu fara da fahimtar inda ta ke a yanzu, da kuma dalilin da ya sa ba ta kai inda mu ke buƙata ta kai ba."

A kan batun aikin wayar da kan jama'a, ya ce aiki ne da ke cikin alhakin da aka ɗora masa a matsayin sa na minista. 
Ya ce, "Mutane su na rage yarda da gwamnati, don haka ya kamata mu tambayi kan mu, ina ne ba mu yi daidai ba? Me ya sa 'yan Nijeriya ba su amince da Nijeriyar ba? Za mu fito da wani tsari na yadda za mu sake fahimtar ko mu su wanene kuma mu fara komawa mu amince da Nijeriya.

"Mutane sun dawo daga rakiyar saƙon da gwamnati ke tura masu. Al'umma ba su tsammanin cewa gaskiya ce gwamnati ke faɗa masu. Ya kamata mu yi abin da zai sa mutane su dawo su na yarda da mu kamar yadda su ke yi a da, kuma mutane su riƙa yarda da aikin da mu ke yi. Dole a riƙa faɗin gaskiya a ko yaushe."

Da ya ke magana kan irin ƙasar da 'yan Nijeriya su ke so su samu, sai ya ce, "Domin amsa wannan tambaya, mu na buƙatar tattaunawa a duk faɗin ƙasar nan kan irin ƙasar da mu ke muradin mu ga mun samu. Me ya sa yanzu a makarantu aka daina wajabta karanta Haƙƙin Ɗan Ƙasa, wato 'Civics'? Wanene ɗan asalin Nijeriya? Shin mun san haka? Akwai buƙatar mu dawo da sanin kyawawan ɗabi'u da aka ɗan mu da su.

"Mun san mu na so mu samu babbar ƙasa nagartacciya kuma mu yarda da muhimmancin mu, a gare mu da kuma ga sauran ƙasashen duniya. Akwai buƙatar mu tattaro kan mu wuri ɗaya don tattauna waɗannan abubuwan, kan rawar da kowanen mu zai taka, da hakkokin da su ka rataya a wuyan mu, da abin da Nijeriya za ta ba 'yan Nijeriya, da kuma abin da su ma 'yan Nijeriya za su ba Nijeriyar."

Bugu da ƙari ya yi tsokaci kan irin 'yancin da jama'ar Nijeriya su ke da shi, ya ce, "Kafafen yaɗa labarai na Nijeriya su na da 'yanci, kuma shi Shugaba Tinubu so ya ke ma ya ƙara masu 'yanci. Yaɗa labarai ya na da muhimmanci wajen samun nasarar kowace gwamnati. Mai girma Shugaban Ƙasa ya na ƙoƙarin faɗin magana a yadda ta ke ba tare da wata ƙumbiya-ƙumbiya ba. 

"Batun yaɗa labaran ƙirƙira da na ƙarya ba matsala ba ce ga Nijeriya ita kaɗai, matsala ce da ta shafi duniya baki ɗaya. Mun ga yadda yaɗa labaran ƙarya ya jawo a Amurka, wanda ya jawo harin ranar 6 ga Janairu da aka kai ainihin cibiyar dimokiraɗiyyar Amurka. Tilas ne mu tunkari matsalar yaɗa labaran ƙarya a duk duniya.

"Bari in ƙara maimaita cewa: Gwamnatin mu ba za ta ƙaƙaba wa kafafen yaɗa labarai ko sauran 'yan Nijeriya takunkumi ba, ko ta yi wa 'yancin 'yan jarida zagon ƙasa. Sai dai kuma ya kamata a sani cewa kowane 'yanci ya na tattare ne da buƙatar mutum ya san alhakin da ke kan sa. 'Yancin tofa albarkacin baki ta na tattare da sanin ya kamata."

No comments

Powered by Blogger.