Cire tallafin mai: Jihar Edo ta ƙara yawan mafi ƙarancin albashi, ta kuma amince da rage kwanakin aiki zuwa uku a mako
Jihar Edo a ranar Talata ta nuna damuwar ta ga halin da 'yan kasa suka samu kansu sakamakon cire tallafin mai wanda ya yi sanadiyyar karin farashin kayayyaki.
Gwamnan jihar, Godwin Obasake, wanda ya ce fararen hula a jihar za su yi aiki kwanaki uku ne a mako ba kwanaki biyar ba saboda karin kudin sufuri, ya bayyana cewa, "Sakamakon cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi, farashin mai ya karu sosai wanda hakan ya haifar da karin tsadar kayayyaki da kuma rashin wadata.
"Gwamnatin jihar Edo ta damu sosai da halin da mutanen mu ke ciki kuma tana tabbatar da cewa tana tare da su a wannan lokaci mai wahala.
"Muna so mu tabbatarwa mutanen mu cewa za mu yi duk abinda za mu iya yi a matsayin gwamnati wajen rage wahalhalu da samar da sauki ga mutanenmu dangane da abinda suke fuskanta yanzu haka.
"A matsayinmu na gwamnati da ke daukar mataki kan abubuwa, tuni mun dauki matakin kara mafi karancin albashi da ake biyan ma'aikatan jihar Edo daga naira 30,000 da aka amince da shi zuwa 40,000 mafi yawa a fadin kasar nan a yau.
"Muna tabbatar maku cewa za mu cigaba da biyan wannan kudin, muna fatar mu kara shi idan kudade masu yawa suka zo jihar mu daga gwamnatin tarayya idan mun yi la'akari da kudaden da za a rinka ajiyewa sakamakon cire tallafin.
"Mun san wahalhalun da wannan shirin ya haifar wanda ya haifar da hauhawar farashin sufuri, kwashe kaso mai yawa na albashin ma'aikata a jihar. Dan haka gwamnatin jihar Edo ta rage kwanakin aiki ga ma'aikata, za su rika zuwa aiki daga kwanaki biyar zuwa kwanaki uku a mako." Kamar yadda gwamnan ya bayyana.
A cikin jawabin, gwamnan wanda ya nemi mutane su kwantar da hankalinsu tare da cigaba da kasuwancinsu kamar yadda doka ta tanada, ya bayyana cewa domin rage kudin wutar lantarki a jihar, gwamnatin jihar za ta cigaba da aiki tare da kamfanonin wutar lantarki a jihar domin kara samar da wutar lantarki ga gidaje da kasuwanci.
Post a Comment