Header Ads

Mutum biyu sun rasa rayukansu, wasu biyar sun raunata sakamakon harbe-harben bindiga a wurin yaye dalibai a jihar Virginia da ke Amurka


Harbe-harben bindiga a wurin da ake yaye daluban wata babbar makaranta da ke Richmond a jihar Virginia ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane biyu da raunata wasu biyar a yayin da harbe-harben bindiga ke kara razana mutane a fadin kasar.

Shugaban 'yan sandan Richmond na wucin gadi, Rick Edward, ya bayyana a ranar Talata cewa wani mutum riki da bindiga ya bude wuta yayin da daruruwan mutane ke tsaye kusa da Monroe Park da ke Richmond bayan an yi bikin yaye dalubai, inda ya kashe mutum biyu tare da raunata wasu biyar.

An dai yi bikin yaye daluban makarantar ta Huguenot High School ne a wani wuri da ake kira Altria Theatre da ke tsallaken titi daga Monroe Park.

'Yan sanda sun kama wani dan shekara 19 da ake zargi wanda ya bar wurin da gudu da kafa, sai dai 'yan sandan Virginia Common Wealth University sun tsayar da shi tare da tsare shi.

'Yan sanda masu bincike sun yi imanin cewa ba ya rasa dangantaka da daya daga cikin wadanda al'amarin ya shafa. Yana da bindigogin hannu guda hudu, uku daga cikinsu da kila an harba su, a tare da shi bayan an kama shi bayan faruwar al'amarin.

Edward ya ce 'yan sanda za su yanke yin caje-caje ne a kan aikata kisa a mataki na biyu bayan wasu laifuffukan ga wanda ya ake zargin.

Kamar yadda Edward ya bayyana, wani dalubi mai shekaru 18 wanda ya kammala karatunsa a ranar Talata da kuma wani mutum mai shekaru 36 wanda ya halarci bikin yaye daluban, duk sun rasu a harbe-harben. Rahoton labarun gidan talabijin din WWBT ya bayyana cewa mutanen da al'amarin ya shafa da ne da mahaifi.

Bayan mutanen biyu da suka rasu, wasu biyar - yaro dan shekara 14 da wasu mutane hudu wadanda shekarunsu ke tsakanin 31 zuwa 58 - sun samu raunuka sakamakon harbin bindigar. Hudu daga cikin wadanda suka raunata din raunin nasu bai ta'azzara ba sosai.

Harbe-harben bindiga dai ya zama ruwan dare a Amurka, wadanda aka kashe da ya shafi harbin bindiga da wadanda suka kashe kansu ya yawaita a kididdiga a shekarar 2021, inda ya kai yawan wadanda suka rasu sanadiyyar bindiga kusan mutum 49,000.

Harbe-harbe a wuraren al'umma kamar makarantu, wuraren siyayya da coci-coci ya razana mutane da dama a Amurka - musamman mata, yara da tsofaffi - a shekarun da suka gabata.

Tun farkon wannan shekarar, an yi harbe-harben bindiga 279 a kasar, kamar yadda Gun Violence Achieve suka bayyana.

No comments

Powered by Blogger.