Header Ads

Iran ta buɗe ofishin jakadancin ta a hukumance a Saudi Arabiya

Ofishin jakadancin Iran da ke Saudiyya

Kasar Iran a hukumance ta bude ofishin jakadancin ta a babban birnin Saudi Arabiya, Riyadh, a ranar Talata, watanni bayan kasashen biyu sun amince su dawo da dangantakar diflomasiyya a tsakaninsu karkashin yarjejeniyar da kasar Sin ta jagoranta.

"Muna kallon yau a matsayin rana mai muhimmanci a dangantakar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da masarautar Saudi Arabiya." Kamar yadda mataimakin Ministan Harkokin Kasashen Wajen Iran, Alireza Bigdeli, ya bayyana a yayin bikin wanda aka yi a hukumance.

"Hadin kai a tsakanin kasashen biyu ya shiga wani sabon mataki." Ya kara da cewa.

Sake bude ofishin jakadancin zai kara karfin tafiye-tafiye a tsakanin Iran da Saudi Arabiya, domin dama suna kokarin dawo da zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye, karfafa safara tare da gina haduwar kasuwanci.

A yayin da Saudi Arabiya ba ta kai ga bude na ta ofishin jakadancin ba a Tehran, dawo da dangantakar diflomasiyyar zai sa alhazan Iran su iya neman bizar zuwa Saudi Arabiya nan-da-nan a Hajji mai zuwa.

Kakakin Ma'aikatar Harkokin Kasashen Wajen Iran, Nasser Kan'ani, ya bayyana a ranar Litinin cewa masu diflomasiyyar Iran tuni suka fara taimakon alhazan kasar Iran dangane da Hajji. Ya bayyana cewa za ma a bude ofishin kasar Iran da ke Jeddah a wannan satin.

A ranar 10 ga watan Maci, bayan kwanaki na sasantawa mai zurfi wadda kasar Sin ta jagoranta, Iran da Saudi Arabiya sun amince su dawo da dangantakar diflomasiyya su tare da bude ofishin jakadancin su bayan shekaru bakwai da lalacewar dangantakar.

A cikin wani jawabi na hadaka da suka fitar bayan sa hannu a yarjejeniyar, Tehran da Riyadh sun nuna bukatar da ake da ita na mutunta junansu a matsayin kasashe tare da gujewa yin shishshighi cikin al'amurran cikin gida na junansu.

Sun amince su tabbatar da yarjejeniyar hadakar tsaro da aka sawa hannu a watan Afirilun shekarar 2001 da kuma wata yarjejeniyar da aka cimmawa a cikin watan Maci na shekarar 1998 na hadaka domin habaka tattalin arziki, kasuwanci, sa jari, fasaha, kimiyya, al'adu, wasanni da al'amurran da suka shafi matasa. 

A watan da ya gabata, Iran ta nada Alireza Enayati a matsayin wakilin Iran a Riyadh. Kafin nan, Enayati ya yi aiki a matsayin Ambasadan Iran a Kuwait, mataimakin ministan harkokin kashen waje da kuma drakta-janar na al'amurran da suka shafi tekun fasha a ma'aikatar harkokin kasashen waje.

A dai ranar 11 ga watan Mayu ne Ministan Harkokin Kasashen Wajen Iran, Hossein Amir-Abdollahian, ya bayyana cewa Saudi Arabiya ta nada sabon ambasada zuwa Tehran, hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da kasar Sin ta jagoranta ne a watan Maci na kasashen su dawo da dangantakar su.

No comments

Powered by Blogger.