Header Ads

Ƙasashen Larabawa da na Musulmai sun haɗa kai wajen yin tir da hare-haren sojojin Isra'ila a Zirin Gaza

Shugaba Tinubu a cikin taron

Taron Haɗin Guiwar Ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashen Musulmai, ya yi tir tare da nuna rashin amincewa kan hare-haren da sojojin Isra'ila ke ci gaba da kaiwa a Gaza.

Taron wanda aka gudanar ranar Asabar, 11 ga Nuwamba, ya bayyana cewa abin da sojojin Isra'ila suka yi laifin tsallake ƙa'idoji da sharuɗɗan yaƙi ne, kuma dabbanci ne kan Falasɗinawa fararen hula.
Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris ne ya tabbatar da haka, a cikin wata sanarwar da Jami'in Yaɗa Labarai na ministan, Rabi'u Ibrahim ya fitar.

Idris, wanda ya na cikin tawagar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu a wurin taron, ya ƙara da cewa kuma an yi kira da a gaggauta gudanar da gagarimin taron duniya, inda za a bijiro da hanyoyin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a yankin Falasɗinu.
Sanarwar bayan taron da wanda shugabannin ƙasashen Ƙungiyar OIC da na Majalisar Ƙasashen Larabawa suka halarta, an yi kira da a gaggauta tsagaita dukkan hare-haren da sojojin Isra'ila ke kaiwa a yankin Gaza. 

Kuma sun fito ƙarara sun ce farmakin da Isra'ila ke kaiwa kan Gaza ci gaba ne da irin mamayar da ta yi wa Falasɗinawa a 1967 a yankin Gaza, West Bank, Al-Quds Al-Sharif da kuma Arewacin Jerusalem.

Sannan kuma taron ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta fito da ƙwaƙƙwarar matsaya a ƙarƙashin Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin, wadda za ta tilasta daina duk wani nau'i da salo na gallazawa da Isra'ila ke yi wa Falasɗinawa.

Haka nan kuma wannan taro ya nemi Isra'ila ta kawo ƙarshen mamayar da ta ke yi a yankin, domin ya karya ƙa'ida da iyakokin da dokokin ƙasa da ƙasa suka shar'anta.

Sun ce musamman farmakin ya saɓa wa ƙa'idar Majalisar Ɗinkin Duniya mai lamba AES-101.25, ta ranar 26 ga Oktoba, 2013.

A wurin taron, shugabannin sun yi kakkausan kira ga Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya cewa "ta gaggauta yin Allah-wadai da dabbacin da sojojin Isra'ila ke kan yi na ruguza asibitoci a Zirin Gaza. Kuma ta yi tir kan hana a shigar wa Falasɗinawa da magunguna, abinci fetur da katse wutar lantarkin da mahukuntan Isra'ila ɗin suka yi a Zirin Gaza."

An zartas da cewa matuƙar Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙi yin tir da dabbancin da sojojin Isra'ila ke aikatawa a Zirin Gaza, to tamkar ta halasta mummunan kisan da ake wa fararen hula ne da suka ƙunshi ƙananan yara, dattawa, mata da kuma ruguza Gaza da ake kan yi.

Sun ce ya zama wajibi Isra'ila ta ɗage takunkumin datse Zirin Gaza da ta yi, tsawon shekaru masu yawa.

Sannan kuma taron ya yi tir dangane da yadda wasu ƙasashe suka riƙa taimaka wa Isra'ila da muggan makaman da take amfani da su, ta na kisan gilla kan Falasɗinawa, tare da ruguza masu gidaje, asibitoci, makarantu, masallatai, coci-coci da sauran wuraren more rayuwa.

No comments

Powered by Blogger.