Header Ads

Gwamnatin Tarayya ta yi fatali da zargin da Peter Obi ya yi mata kan ɗorin kasafin kuɗi

Shugaba Bola Ahmad Tinubu 

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce ɗorin kasafin kuɗi na shekarar 2023 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu a ranar Laraba, 8 ga Nuwamba, 2023 ba a yi shi cikin rashin tunani da hangen nesa ba, an yi shi ne bisa la'akari da halin matsin tattalin arziki wanda Nijeriya ta ke fuskanta a yanzu. 

A wata takarda ga manema labarai da ya rattaba wa hannu a ranar Alhamis, hadimin ministan na musamman a ɓangaren yaɗa labarai, Malam Rabi'u Ibrahim, ya ruwaito cewa ministan ya yi kira ga ɗan takarar zama shugaban ƙasa na Jam'iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya samu lokaci ya zauna ya karanta kundin ɗorin kasafin kuɗin na naira tiriliyan 2.17 a tsanake domin ya fahimce shi da kyau, zai ga ya ƙunshi tanadin kuɗin da aka yi wa muhimman ayyuka irin su tsaro, aikin gona, wadata ƙasa da abinci, ayyuka da gidaje, ƙarin albashi ga ma'aikata, shirin bada rance ga ɗalibai, da hanyoyin sauƙaƙa wa talaka halin da ya ke ciki, da sauran su, waɗanda an yi su ne don a ƙarfafa ginshiƙin tattalin arzikin ƙasar tare da inganta halin zamantakewa a tsakanin 'yan Nijeriya.

Ya ce: “Ɗimbin tanade-tanaden da ke cikin ɗorin kasafin kuɗin ya nuna babban burin Shugaba Tinubu da yadda ya ke matuƙar son ya tallafa wa ayyukan da gwamnati ta sa a gaba, ya tunkari matsalar tsaro gaba-gaɗi, kuma ya gaggauta haɓaka hanyoyin da za a bi a magance matsalolin ƙasar waɗanda cire tallafin mai ya haifar.

Idris ya yi kira ga 'yan siyasar adawa da su kasance masu sani kuma adalai wajen bayyana ra'ayin su mabambanta, sannan su kauce wa yi wa gaskiya jirwaye don kurum su cimma burin siyasa. 

Ya yi bayanin cewa an yi ɗorin kasafin kuɗin ne bayan tattaunawa tare da tuntuɓar masu ruwa da tsaki da su ka dace waɗanda su ka bada tabbacin cewa kasafin ya yi daidai da buƙata da muradun jama'ar Nijeriya.

Idris ya nanata cewa kamar yadda Shugaba Tinubu ya ke da son ganin an bi dukkan ƙa'idoji wajen sarrafa kuɗin gwamnati, to sai da aka yi nazari a tsanake kan kowane lissafi a kasafin kuɗin don tabbatar da cewa an kashe kuɗaɗen jama'a a yadda ya kamata.

No comments

Powered by Blogger.