Header Ads

Ku nesanci 'yan siyasa ko shiga gidan gwamnati - Gargaɗin INEC ga sabbin kwamishinonin zaɓe



Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya gargaɗi sababbin kwamishinonin zaɓe cewa su nisanci shiga harkokin siyasa ko yin tarayya da 'yan siyasa, sai fa  a bisa ƙa'idar da doka ta tanadar.

Yakubu ya bukace su da tabbatar su na bin dukkan tsare-tsaren da dokar zaɓe ko dokar ƙasa ta shimfiɗa wajen gudanar da aikin su.

Shugaban ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da ya ke rantsar da sababbin Kwamishinonin Zaɓe 19.

Ya ce ya zama tilas su kasance su na aiwatar da komai a bisa ƙa'ida, ba tare da nuƙu-nuƙu ko fifita wani ɓangare ba.

Yakubu ya ce: "Kuma a duk lokacin da ku ke ganawa da masu ruwa da tsaki, to ku kasance ba ku wuce ƙa'idar da dokar ƙasa ta gindaya maku.

"Haka ma a yayin tuntuɓar juna tsakanin ku da jama'a, kada ku tsallake iyakokin da dokar ƙasa ta hana ku tsallakawa.

"Sannan ku nisanci kai ziyara ofishin gwamna. Wato ba a son a gan ku gidan gwamnati. Kuma kada su riƙa keɓewa ku na ganawa da 'yan siyasa ba bisa ƙa'idar aikin ofis ba. Ko bayan tashi daga ofis, ba a yarda su riƙa keɓancewa da 'yan siyasa ba.

"Ku tuna gwamnatin tarayya ku ke wa aiki, saboda haka ita ce abin biyayya a gare ku. Don haka kada ku kauce daga turba, gudun kada ku kai ga zubar da ƙimar ku da darajar INEC.

"Kuma ina ƙara jaddada maku cewa hanyar amfani da tsarin tantance sahihiyar rajistar zaɓe ta BVAS ce kaɗai hanyar da aka amince a tantance mai rajistar zaɓe."

Daga cikin sababbin kwamishinonin da Yakubu ya rantsar akwai Uzochukwu Chijoke a Jihar Abiya, Nuru Inusa a Adamawa, Elizabeth Agu a Anambara, Mahmood Nura a Bauchi, Samuel Egu a Binuwai, Yomere Otitsemolebi a Kuros Riba da Onyeka Ugochi a Ebonyi.

 Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya na gaisawa da daya daga cikin sababbin kwamishinonin zaɓen da aka rantsar

No comments

Powered by Blogger.