Header Ads

Gargaɗi daga INEC: A guji wata manhajar bogi da aka buɗe da ƙaryar ana ɗaukar ma'aikatan zaɓen 2023

Wani gargaɗin baya-bayan nan daga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ja kunnen jama'a cewa ba ta san da zaman wata manhajar da wasu 'yan damfara su ka buɗe da sunan ɗaukar ma'aikatan zaɓe na wucin-gadi ba.

Sakataren Yaɗa Labaran INEC, Rotimi Oyekanmi ne ya yi wannan gargaɗin, ranar Talata a Abuja.

Ya ce tuni INEC ta rufe shafin manhajar ta na ɗaukar ma'aikatan zaɓe, kamar yadda ta yi bayani a baya.

A cikin Satumba ne dai INEC ta yi sanarwar cewa za ta buɗe shafin manhajar a ranar 14 ga Satumba, 2022 ta rufe a ranar 14 ga Disamba, 2022.

"Wannan shafin manhaja na intanet, na bogi ne, ba na INEC ba ne. Saboda an rufe shafin manhajar INEC na ɗaukar ma'aikatan wucin-gadi, tun a ranar 14 ga Disamba, 2022."

Oyekanmi ya bayyana sunan manhajar ta bogi da: URL-http://www.yournewclaims.com/INEC/recruitment, cewa ta bogi ce kawai kuma a nesance ta.

A wani labarin kuma an samu tabbacin cewa akwai katin rajistar zaɓe har milyan 6.7 da har yanzu ba a karɓa ba a cikin wasu jihohi 17.

Rashin karɓar katin da aka yi rajista dai na ɗaya daga cikin abin da ke haifar da matsalar rashin zuwa a jefa ƙuri'a, kamar yadda INEC ta tabbatar cewa a zaɓen 2019 mutum miliyan 82 ne ke da rajistar zaɓe, amma mutum milyan 28.6 kaɗai su ka fita su ka jefa ƙuri'a.

Duk da yawan masu jefa ƙuri'a a Jihar Legas, waɗanda su ka yi zaɓe a jihar ba su cika miliyan biyu ba.
Shugaban INEC 

No comments

Powered by Blogger.