Header Ads

Zaɓen 2023: INEC za ta ɗauki ma'aikata milyan 1.4 domin horar da su yadda za su yi amfani da na'urar BVAS - Okoye

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce ta fara shirye-shiryen ɗaukar ma'aikatan wucin-gadi domin fara horas da su yadda za su yi aiki da na'urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, wato BVAS.

Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka a wata tattaunawa da akayi da shi ƙarshen makon jiya, a gidan talbijin na Channels TV.

Ya ce akwai buƙatar bayar da horon ƙwarewa wajen yin amfani da BVAS ɗin, ta yadda a lokacin zaɓuka ba za a riƙa samun jinkiri ba, wanda hakan ka iya sa masu jefa ƙuri'a yin ƙorafi da tsarin tantance su ta hanyar amfani da BVAS ɗin.

Okoye ya ce za a wadatar da BVAS a dukkan rumfunan zaɓe 176,846 da ke faɗin ƙasar nan.

Wani bincike kuma, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar har yanzu akwai aƙalla mutum milyan 1.7 da ba su karɓi katin shaidar rajistar zaɓe ba, wato PVC, a Jihar Legas.

Rahotanni sun nuna cewa ya zuwa ranar Asabar, mutum 5,816,528 ne su ka karɓi shaidar rajistar zaɓe a Jihar Legas.

Tuni dai Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara kokawa da yadda karɓar katin shaidar rajistar zaɓe ke tafiyar-hawainiya a wasu jihohin, ganin yadda jama'a ba su bayar da himma sosai wajen tururuwar zuwa a karɓi katin, wanda sai da shi ne mutum zai iya jefa ƙuri'a a zaɓukan Nijeriya.

Hakan ya sa cikin makon jiya INEC ta je Jihar Cross River, inda ta riƙa wayar wa jama'a kai cewa su hanzarta su je su karɓi katin shaidar rajistar zaɓen su.

Hukumar ta yi wannan kiran ne a wurin gagarimin taron kalankuwar 'Calabar Carnival'.

A Jihar Akwa Ibom ma hukumar ta koka ganin yadda jama'a ba su yin tururuwar zuwa karɓar katin shaidar rajistar zaɓe.

A Gundumar Babban Birnin Tarayya (FCT) kuwa, rahotanni sun nuna cewa har yanzu akwai katin shaidar rajistar zaɓen da ba a karɓa ba, tun daga 2011 zuwa 2022, har guda 460,643.

Rahotannin sun nuna cewa daga 2011 zuwa 2019 akwai katin da har yanzu ba a karɓa ba, guda 230,007.

Sai kuma waɗanda aka yi wa rajista amma ba su karɓa ba daga 2021 zuwa 2022 har guda 230,636.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels, Kakakin Yaɗa Labaran INEC, Festus Okoye, ya jaddada cewa INEC za ta yi amfani da na'urar tantance mai rajistar katin zaɓe, wato BVAS a dukkan rumfunan zaɓen ƙasar nan guda 176,846.

Sannan ya ce tuni INEC ta fara aikin yadda za ta ɗauki ma'aikatan wucin-gadi fiye da milyan 1.4 waɗanda za a bai wa horon aiki da na'urar BVAS a lokacin zaɓukan shugaban ƙasa, na 'yan majalisar tarayya, gwamnoni da na majalisar dokoki ta jihohi.
Hoto: Farfesa Yakubu, Shugaban INEC

No comments

Powered by Blogger.