Header Ads

Tinubu bai da lafiyar ƙwaƙwalwa da har zai iya mulki, inji Naja'atu Mohammed bayan ta koma wajen Atiku

Ɗan takarar zama shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, bai da isasshiyar lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa da har zai iya riƙe muƙamin shugabancin Nijeriya, inji tsohuwar jigo a jam'iyyar, Hajiya Naja'atu Mohammed.

Haka kuma Tinubu bai da wani shiri da ya yi na taimaka wa Arewa ta kowace fuska, inji ta.

Hajiya Naja’atu, wadda 'yar asalin Kano ce, ta faɗi haka ne a wata hira da jaridar The Whistler ta yi da ita a yau.

Hajiya Naja, kamar yadda ake kiran ta, an san ta da feɗe gaskiya komai ɗacin ta.

Ranar Asabar da ta gabata ne ta yi murabus daga rundunar yaƙin neman zaɓen Tinubu inda ta riƙe muƙamin darakta mai kula da ƙungiyoyin sa-kai.

A wasiƙar murabus ɗin, wadda ta tura wa Shugaban APC na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, Naja'atu ta ce abubuwan da ke faruwa a cikin 'yan kwanakin nan a fagen siyasar Nijeriya sun sanya ta ga cewa ba za ta iya ci gaba da yin siyasar kowace jam'iyya ba. 

Ta ce ta gwammace ta taka rawar siyasar ta ta fuskar yin gwagwarmayar tabbatar da mulki mai nagarta don gyara ƙasar nan.

Sai dai kuma washegari, Lahadi, ta kai wa Atiku ziyara a gidan sa inda ta bayyana cewa ta koma goyon bayan takarar sa.

A hirar ta da jaridar The Whistler, 'yar siyasar ta yi ƙarin bayani kan ainihin dalilan ta na barin Tinubu, ta ce ɗan takarar na APC ya bayyana ƙarara cewa ya na fama da ciwon mantuwa lokacin da ta ziyarce shi a London.

Ta ce: “Asiwaju da na zauna da shi, a yawancin lokacin duk barci ya ke yi, a gaskiya Bisi Akande ne na ke magana da shi. Abu mai muhimmanci shi ne ba wai kawai bai da ƙosasshiyar lafiyar jiki kaɗai ba ne, bai ma da lafiyar ƙwaƙwalwa. Ko mu na so, ko ba mu so, gaskiyar maganar kenan.

"Ba wai ba na ƙaunar sa ba ne, a'a, ina girmama shi domin na ji labarin mutum ɗaya ko biyu da ya taimaka wa a rayuwa, wanda hakan ya dace. To amma idan ka na zancen shugabancin sama da mutum miliyan ɗari biyu, ka san cewar idan ka cire ra'ayin ƙabilanci to ba zai iya ba, kawai wasu da ke zagaye da shi ne za su yi mulkin. Zahirin lamarin kenan. Ya na da taɓin hankali – ni na faɗa!

“Na zauna tare da shi tsawon awa biyu a London, idan ka yi maganar tsanwa, shi sai ya ba ka amsar ja. Ba ya ma iya raba ɗaya biyu. Ya na da tsananin ciwon mantuwa. Na tabbatar ya na da ciwon sankarar tsufa, wato Alzheimer’s, domin hatta kofin shayi bai iya riƙewa. 

“Idan fa ka cire ra'ayin ƙabilanci, idan ka cire jaridun Legas da Ibadan, in da a ce Tinubu ba Bayarabe ba ne, to bai isa ya fito takarar zaɓe ba domin za su yi raga-raga da shi ne. To amma ga mutane nan jingim su na ta kare shi don kawai Bayarabe ne, ana faɗin 'ai namu ne, egbe omo Oduduwa, hakan ya fi komai'."

Hajiya Naja, wadda shekarun ta 66 a bana, ta ci gaba da cewa: “Tare da ni aka je kamfen na Yola, har sai da mu ka roƙe su da su karɓe makirfon daga hannun sa.

"Duk wani abu game da Tinubu an gina shi ne bisa ƙarya. Ka ɗauka cewar Bahaushe ne, shin zai iya yin takara da duk waɗannan matsalolin da ke tattare da shi? A wannan yaƙin neman zaɓen kada wanda ya yi maganar yaƙi da cin hanci da rashawa domin dukkan su su ne fuskar cin hanci da rashawar.”

Bugu da ƙari, Naja'atu Mohammed ta bayyana cewa Tinubu bai yi komai ba domin taimakon Arewa duk da ɗimbin matsalolin da su ka addabi yankin. Ta tuno da wata magana da ta yi masa a lokacin haɗuwar da ta yi da shi a London. Ta ce: “Na tambayi Tinubu, 'Wane tanadi ka yi mana mu a Arewa?' Sai ya kalle ni a tsabar ido na ya ce, “Ba wani abu.' Na ce masa, 'Ran ka ya daɗe, ka na nufin babu wani shiri da ka yi wa Arewa? Ga matsalar tsaro, yaran da ba su zuwa makaranta, aikin gona, da wasu masu yawa irin waɗannan, kowa a arewa-maso-gabas na jiran a kashe shi ko a yi kidinafin ɗin shi?”

A cewar ta, ita dai ba ta ƙara yin tozali da Tinubu ba tun daga lokacin da ta karɓi muƙamin da aka ba ta a rundunar yaƙin neman zaɓen sa.

Da aka tambaye ta ko ta na ganin Shugaba Muhammadu Buhari ya na goyon bayan Tinubu? Sai ta amsa da cewa: Buhari ba ya goyon bayan kowa; son ran sa ya yi yawa, ka ce Ni na faɗa maka, Buhari bai taɓa goyon bayan kowa ba sai kan sa kaɗai. 

"Zan yi matuƙar mamaki idan ya na goyon bayan shi, kuma idan Buhari na goyon bayan wani to babu abin da wannan mutum zai samu. Saboda haka, da na ji Asiwaju ya ce zai ɗora a inda Buhari ya tsaya, cewa na yi, 'Ka kashe kan ka a Arewa' saboda ba a son Buhari. Je ka duba kasafin kuɗin sa a tsawon shekarun nan, abin da ya fi ware wa kuɗi mafi girma a arewa-maso-yamma shi ne kashi 12 cikin ɗari, kuɗin da ya fi ware wa harkar gona shi ne kashi 2, kuma ana ƙin jinin sa saboda bambancin da ya ke nunawa. Dukkan hafsoshin soja da 'yan sanda, har da hukumar kwana-kwana, 'yan Arewa ya naɗa, kuma sai ya naɗa marasa amfani daga cikin su, saboda a ci gaba da kashe mu don ka riƙa cewa ɗan'uwan ka ne ke kashe ka. To, idan ɗan'uwan ka ne ke kashe ka menene bambancin ga wanda abin ya shafa? Yanzu maganar da ake yi, ana can ana sace mutane a Katsina, babu ranar da ba a sace mutane a jihohin Katsina da Zamfara da Neja.  Saboda haka, idan an ce Fulani ko ba Fulani ba ne, wa ya damu? Idan daga sama ka faɗo amma kai shugaba ne da ya cancanta, mecece samuwar a wurin da ya dace?

"Amma Nijeriya ta zama mallakin masu mulki. In da a ce Osinbajo aka tsayar, na rantse da Allah da na ba da rayuwa ta saboda Osinbajo, domin shi ne ya fi cancanta, mutum ne a buɗe, ya na da himma, kuma ya na saka ido a kan komai sannan ya na kallon Nijeriya baki ɗayan ta. A 'yan watannin da ya riƙe ƙasar, ya canja abubuwa da dama. Saboda haka, saboda me zan saka ra'ayin son zuciya. In da Yarabawa da gaske su ke me ya sa ba su kawo Osinbajo ba, wanda fasto ne? Ka zo ka na tikitin Muslim-Muslim a yanzu. Annabi mai tsira da aminci ya ce kafiri ya fi Musulmin da bai yin adalci. To, don me zan damu da wani Muslim-Muslim? To amma sun dage wajen yin gangamin mutane a fagen siyasa amma kuma su na yaudarar jama'a ne. Wane Musulunci su ke yi? Mutumin da ko Fatiha bai iya karantawa, shi ke kiran kan shi Musulmi. Idan ba ka karanta Fatiha ba, ba ka da sallah, wanda ya nuna ba ya ma sallah kenan. Wane irin shashanci ne wannan? Ba ruwa na da wani zancen tikitin Muslim-Muslim, to amma saboda Nijeriya ƙasa ce ta jahilci, an kai tumaki mayanka, shi ya sa masu mulki su ka hana 'ya'yan talaka su yi ilimi, musamman a Arewa."

Hajiya Naja ta bayyana cewa ita yanzu ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP, wato Atiku Abubakar, za ta goya wa baya a zaɓen da za a yi domin gara shi da Tinubu.

Ta ce: “Abin da zan ce shi ne idan aka ce in zaɓi ɗayan biyu a tsakanin wani mugun abu da wani mugun abin, to Atiku zan bi, domin kuwa ko ba komai dai na bi inda hankali na zai kwanta. Ba domin son rai na na ke yi ba, ina yi ne saboda Allah kuma saboda ƙasa ta.”
 Hajiya Naja'atu Mohammed tare da Atiku Abubakar da kakakin kamfen ɗin Atiku, Sanata Dino Melaye, a gidan Atiku a Abuja a ranar Lahadi

No comments

Powered by Blogger.