Header Ads

Canjin kudi: Me ya sa Gwamna Ganduje ya kai karar Buhari kotun koli?

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje

Gwamnatin jihar Kano ta shigar da karar shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis kan sauyin fasalin kudi na naira 200, 500 da kuma 1000.

Wannan kara dai ta gwamnatin Kano, wadda Babban Layaun jihar Kano ya shigar ta hannun babban lauya a Nijeriya, Sanusi Musa (SAN), na neman kotun kolin ta ayyana cewa shugaba Buhari shi kadai ba ya da ikon umartar babban bankin Nijeriya dakatar da amfani da takardun kudin na 200, 500 da kuma 1000 ba tare da tuntubar majalisar tattalin arzukin kasa da kuma majalisar zartarwa ta kasa ba.

Gwamnatin ta jihar Kano ta bukaci kotun da ta soke matakin babban bankin Nijeriya na janye takardun kudin na 200, 500 da 1000 inda ta bayyana cewa janyewar ya shafi tattalin arzukin mutanen jihar mutum miliyan 20.

Bayan haka gwamnatin na neman kotun kolin da ta bayar da umarnin da zai tilastawa gwamnati soke shirin ta na sauyin kudin, domin a cewar ta ya sabawa tsarin mulkin kasar na shekarar 1999.

Hakazalika gwamnatin na bukatar kotun kolin ta Nijeriya da ta zartar cewa umarnin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba babban bankin na takaita yawan kudin da jama'a za su fitar daga asusunsu na banki ba tare da tuntubar majalisar tattalin arzuki da kuma majalisar zartarwa ba, abu ne da ya sabawa tsarin mulki, ya kuma sabawa doka saboda haka saboda haka ba shi da iko.

Dama dai ko kafin gwamnatin ta jihar Kano ta shigar da kara kotun kolin, gwamnatocin arewacin Nijeriya uku da suka hada da Kaduna, Kogi da Zamfara sun shigar da kara kan al'amarin canjin kudin, inda har kotun ta dakatar da babban bankin aiwatar da wa'adin da ya sa na 10 ga watan Fabrairu ga tsofaffin kudin har sai ta yanke hukunci a ranar 15 ga watan na Fabrairu.

No comments

Powered by Blogger.