Header Ads

Masu garkuwa da mutane sun nemi a biya su naira miliyan 150 domin sako kwamishinar matan jihar Kuros Ribas

Gwamnan jihar Kuros Ribas, Ben Ayade

Bayan kwashe kwanaki takwas a tsare, masu garkuwa da mutane a jihar Kuros Ribas sun nemi a biya su naira miliyan 150 domin sakin kwamishiniyar matan jihar, Farfesa Gertrude Njar. 

Mawallafin Cross Rivers Watch, Agba Jalingo, ne ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumunta ta Facebook.

Kwamishiniyar dai an sace ta ne a kan titin Mayne Avenue-Atamunu a kusa da Calaba South a farkon awowin ranar 1 ga watan Fabrairu. 

Jaridar The Punch ta ruwaito kwamishinan yada labarai na jihar, Eric Anderson, a yayin hirar sa da 'yan jaridu kan wannan al'amari, na bayyana cewa 'yan sanda da kuma Babban Sakataren Ayyuka na Musamman, Dakta Alfred Mboto, duk an tuntubesu, tare da bayyana damuwarsa a kan yadda wannan irin mummunan al'amari zai iya faruwa a tsakiyar cikin gari.

Gwamnan jihar, Ben Ayade, shi ya rantsar da Farfesa Gertrude Njar tare da sauran kwamishinoni ba da dadewa ba.

No comments

Powered by Blogger.