Header Ads

Isra'ila ta kashe Falasdinawa akalla 31, ta rusa gine-gine da dama cikin makonni uku - Majalisar dinkin duniya

Wasu sojojin HKI sun sintiri

Majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa Isra'ila ta kashe faladinawa da dama tare da ko dai rushewa ko kwace gine-ginensu da dama a cikin makwanni uku a cikin watan Janairun shekarar 2023.

Ofishin majalisar dinkin duniya na bayar da tallafi, Office for the Coordination of Humanitarian Affairs (OCHA) da ke Falasdin ne ya bayar da kididdigar a cikin rahotonsa na duk bayan sati biyu na kariya ga fararen hula, daga 10 zuwa 30 ga watan Janairu kamar yadda official Palestinian Wafa news agency ta wallafa a ranar Asabar.

Kamar yadda rahoton ya nuna, kashe-kashen da raunukan sun hada da wadanda suka afku yayin wani kutse da Isra'ilan ta yi a ranar 26 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10 a birnin Jenin kusa da wani sansanin 'yan gudun hijira a arewacin kogin Jordan. Wadanda suka rasu a wannan lokacin, wanda ya hada da yara biyu da mace daya, sun kasance mafi yawa tun shekarar 2005 lokacin da OCHA ta fara tattara bayanan Falasdinawa da suka jikkata.

Gaba daya dai, Falasdinawa 441 wadanda suka hada da yara 49 sojojin Isra'ila suka jikkata a cikin wannan lokaci, kamar yadda rahoton ya bayyana, inda ya kara da cewa 74 a cikin su, wato kashi 18 cikin 100, sojojin Isra'ila sun farmakesu ne da harsasai masu rai.

Bayan haka, mazauna yankunan 'yan kasar Isra'ila sun jikkata Falasdinawa 18 har da karamin yaro a cikinsu, a lokuta daban-daban har tara, sun kuma lallata kadarorin Falasdinawa a lokuta daban-daban har sau 42.

A cikin dai wannan lokaci, hukumomin na haramtacciyar kasar Isra'ila sun rushe tare da kwace gini-gine na Falasdinawa har 88 a daukacin fadin wuraren da suka mamaye.

A sakamakon haka, Falasdinawa 99 da suka hada da yara 54 sun rasa muhallansu, hakan ya shafi muhallin wasu Falasdinawan su 21,000 kamar yadda rahoton ya bayyana.

Sama da Falasdinawa miliyan uku ne dai ke zaune a yamma da gabar kogin Jordan da kuma gabashin al-Quds wanda Isra'ila ta mamaye tun shekarar 1967, bayan sun kaddamar da yaki a kan Falasdinawa tare da taimakon yammacin duniya.

Tun bayan wannan mamaya kuma, Isra'ila ta cigaba da gina daruruwan gine-ginen ta wadanda ba kan ka'ida suke ba a kowanne bangare na yamma da kogin Jordan, wanda a yanzu ya ke dauke da dubunnan daruruwan mazauna 'yan kasar ta Isra'ila.

Kamar yadda kididdiga ta bayan nan ta nuna, mazauna 'yan Isra'ila da ke yamma da kogin Jordan sun fi mutum dubu dari biyar.

No comments

Powered by Blogger.