Header Ads

Tsohon shugaban kasar Pakistan, Pervez Musharraf, ya rasu

marigayi Musharraf

Tsohon shugaban kasar Pakistan, Pervez Musharraf, wanda ya kwace mulki yayin wani juyin mulki a shekarar 1999, ya rasu yana da shekaru 79 a duniya sakamakon wata jinya mai tsawo.

Tsohon shugaban, wanda ya yi mulki a tsakanin shekarun 2001 zuwa 2008, ya tsallake hare-haren yunkurin hallaka shi da dama inda daga baya ya tsinci kansa a tsakanin dambarwar da ake yi a tsakanin masu tsattsauran kishin musulunci da kuma kasashen yamma.

Marigayin, wanda ya fadi zaben shekarar 2008 tare da ficewa daga kasar wata shida bayan haka, ya goyi bayan "yaki da ta'addanci" wanda kasar Amurka ta kaddamar bayan harin 9/11 duk da adawa da hakan da 'yan kasarsa suka nuna.

Saidai an kama tsohon shugaban tare da yanke masa hukuncin kisa a bayan idonsa daga baya kuma aka janye hukuncin, hakan kuwa ta faru ne bayan ya koma kasar domin tsayawa takara a shekarar 2013.

Marigayin ya koma Dubai da zama a shekarar 2016 don yin jinya a can. Tun daga lokacin ne kuma ya ke yin zaman gudun hijira wajen kasarsa.

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif da shugaban kasar ta Pakistan, Arif Alvi, duk sun mika ta'aziyyarsu ga iyalan mamacin, a yayin da rundunar soja ta mika ta'aziyyarta tana mai cewa, "Allah ya yi wa mamacin albarka kuma ya baiwa iyalansa hakurin rashi."

No comments

Powered by Blogger.