Header Ads

Zaɓen 2023: Al'ummar Ibo na Kano sun ce Atiku ne ya fi dacewa da shugabancin Nijeriya


Hoto: Eze Ikechukwu Akpudo da Alhaji Ibrahim Al-Amin (Little) a lokacin ziyarar a fadar Sarkin al'ummar Ibo na Kano

Al'ummar Ibo mazauna Jihar Kano sun bayyana goyon bayan su ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, a babban zaɓen da za a yi a wannan watan.

Sarkin Ibo na Kano, wato Eze Ikechukwu Akpudo, shi ne ya bayyana haka a madadin al'ummar tasa a lokacin da sarkin yaƙin rundunar zaɓen Atiku a Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ali-Amin (Little), ya kai masa ziyara a fadar sa.

Eze ɗin ya bayyana Atiku da cewa wani kadarko ne wanda ya yi aiki matuƙa wajen kawo haɗin kai a ƙasar nan.

Ya ce: “'Yan Nijeriya ba su da zaɓin da ya wuce Atiku, domin shi kaɗai ne wanda zai iya doke Tinubu a zaɓe. Ya na takara a babbar jam'iyya. 

"Wani dalilin kuma shi ne ba za mu iya goyon bayan tsarin takarar Muslim-Muslim ba. Mu na so a samu takara mai daidaito domin tabbatar da adalci ga kowa da kowa.

“Kamar yadda ku ke gani, kwanaki kaɗan ne su ka rage kafin a yi zaɓe, amma babu wani daga cikin mu da zai tashi ya koma garin su domin yin zaɓen. A nan za mu yi zaɓen tare da iyalan mu. Nan za mu tsaya, a nan mu ke harkokin kasuwancin mu.

“Addu'ar mu ita ce a yi zaɓe cikin lumana. Mun yanke shawarar cewa Atiku Abubakar kaɗai ne zai iya tunkarar matsalolin da ƙasar nan ke fuskanta a yau.

“Mu na magana ne da murya ɗaya a matsayin mu na al'umma ɗaya. Ba mu yin wata ƙunbiya-ƙunbiya a magana, kuma mu na ba mai girma Atiku tabbacin cewa shi za mu ba ƙuri'un mu. 

“Ni ɗin nan sau biyu ana zaɓa ta a matsayin kansila a Sabon Gari. Zan tattaro jama'a bakin iyawa ta don ganin Atiku ya samu nasarar lashe zaɓen da za a yi."

A nasa ɓangaren, Ali-Amin Little ya bayyana cewa 'yan ƙabilar Ibo mutane ne masu son zaman lafiya kuma sun yi fice a harkar kasuwanci.

Ya yi kira a gare su da su yi amfani da ƙuri'ar su yadda ya kamata domin su samu cin moriyar mulkin dimokiraɗiyya tare da sauran al'umma.

Ya ce: “Atiku Abubakar zai yi tafiya tare da dukkan ƙabilu idan ya zama shugaban ƙasa. Ƙasar nan ta yi masa komai na rufin asiri, don haka shi ma ya ke so ya mayar mata da sakayyar alheri ta hanyar samar da shugabanci mai nagarta da alfanu ga 'yan Nijeriya.

“Hakan ne ya sa ya ke auren mace Ibo, da Bayarabiya da Kanuri, da sauran su. Shi Waziri mutum ne da ya kamata 'yan Nijeriya su amince da shi saboda amfanuwar ƙasar da haɗin kan ta.”

Wasu waɗanda su ka take wa Al-Amin Little sawu a lokacin ziyarar sun haɗa da Dakta Auwalu Anwar, wanda shi ne mai ba Atiku shawara a ɓangaren tsare-tsare, da kuma Alhaji Bashir Kalla.


No comments

Powered by Blogger.