Header Ads

Me ya sa Chadi ta bude ofishin jakadancinta a Isra'ila?

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu tare da shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, bayan bude ofishin jakadancin kasar Chadi a birnin Tel Aviv

Firaministan haramtacciyar kasar Isra'ila, Benjamin Netanyahu, tare da shugaban kasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, a safiyar ranar Alhamis 2 ga watan Fabrairun shekarar 2023 sun hadu domin bude ofishin jakadancin Chadi a Tel Aviv, wani al'amari da shugabannin biyu suka kira da "babban al'amari a tarihi."

A shekarar 2019, Benjamin Netanyahu da mahaifin shugaban kasar ta Chadi wanda ya rasu, Idriss Deby Itno, suka sanar da daidaita alakar diflomasiyya da ke tsakanin su. Chadi dai ta yanke alakar ta da Isra'ila ne tun shekarar 1972 biyo bayan takurawa daga shugaban kasar Libiya, marigayi Muammar Gaddafi.

Idriss Deby Itno, wanda ya mulki kasar Chadi kusan shekara 30, kuma wadda kasa ce da mafi yawanta musulmai ne, ya rasu ne a shekarar 2021 a filin yaki da 'yan tawaye, inda dansa ya maye gurbinsa a matsayin shugaban kasa kuma shugaban sojoji.

"Wannan wani yini ne mai cike da tarihi, wannan ya biyo bayan matsayar da muka dauka ni da mahaifinka marigayi, zuwa na kasar Chadi mai cike da tarihi da kuma zuwan ka Isra'ila a yau, inda muke bude ofishin jakadanci a hukumance a yau," kamar yadda Netanyahu ya bayyana

Shima a nasa bangaren, shugaban kasar ta Chadi ya bayyana cewa wannan rana ce mai matukar tarihi ga kasar ta Chadi da Isra'ila, inda ya bayyana sadaukar da wannan yini ga mahaifinsa, "Mutum jarumi mai hangen nesa" kamar yadda ya bayyana.

Bayan sauka kasar Isra'ila, Mahamat Idriss Deby ya samu tarba tun daga filin saukar jiragen sama daga shugaban kungiyar leken asirin Isra'ila ta MOSSAD, David Barnea, sai kuma tawagar ta kasar Chadi ta nufi cibiyar ta MOSSAD domin gudanar da tattaunawa da bikin murna.

MOSSAD ta yi aiki tukuru wajen ganin alaka ta dawo daidai da kasar Chadi tun bayan shekarar 1972, tare da aiki a cikin shekarun nan domin ganin daidaituwar alakar, "Muna cike da fata cewa wasu kasashen na Afirka da gabas ta tsakiya za su yi koyi da wannan babbar yarjejeniya kuma su kyautata alakarsu da Isra'ila." Kamar yadda shugaban na MOSSAD, David Barnea ya bayyana.

No comments

Powered by Blogger.