Header Ads

Sabuwar Naira: Daruruwan mutane sun fito zanga-zanga a Legas saboda karancin kuɗi

An gudanar da wata babbar zanga-zanga ta daruruwan mutane a ranar Alhamis a Marina, Lagos Island, da ke jihar Legas sakamakon rashin isassun sabbin kudi da wahalhalun da jama'a suka fada a sakamakon hakan.

Akwai dai rashin isassun sabbin kudin a kusan kowane bangare na Nijeriya, inda mutane ke korafin rashin sabbin kudin domin sayen abinci, yin tafiye-tafiye da sauran al'amuran yau da kullum.

Wannan na zuwa ne a yayin da ba a iya samun sabbin kudaden daga na'urorin cire kudi na ATM da bankuna.

Zanga-zangar ta Legas dai gamayyar kungiyoyin fararen hula ne suka shirya ta, inda daruruwan mutanen da suka fito suka taru a bankunan da ke tsibirin suna wake-waken neman sai an ba su sabbin kudaden.

Mai magana da yawun kungiyar a yayin da yake jawabi a cikin wani bidiyo ya bayyana cewa, "A yanzu muna a kofar bankin Wema, mun baro bankin UBA, duk sai mun je cibiyoyin bankunan dukkan su.

"Sabbin kudaden namu ne dukan mu. Mun je na'urar cire kudi ta ATM ba mu iya samun sabbin kudin ba, mun je bankuna ba mu iya samun sabbin kudin ba.

"Mun san cewa babban bankin Nijeriya ya samar da kudaden ga bankuna, wannan shi ya sa kungiyoyin fararen hular suka ga ya kamata su je bankuna su fada masu su daina wahalar da 'yan Nijeriya."

No comments

Powered by Blogger.