Header Ads

Me ya sa 'yan sanda suka kama mutane 35 magoya bayan Atiku Abubakar a jihar Ribas?

Alhaji Atiku Abubakar na PDP

'Yan sanda a cikin motoci kusan shida sun afka cikin wani taro na magoya bayan dan takarar shugaban kasar Nijeriya a karkashin jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, wanda taro ne wadanda Atiku Support Organization (ASO) suka shirya a jihar Ribas, tare da kama mutane 35. 

Sakataren yada labarai na kungiyar ta ASO, Dakta Victor Moses, wanda ya zargi gwamnan jihar ta Ribas, Nyesom Wike da aiwatar da kamen, ya bayyana cewa al'amarin ya faru ne da misalin karfe 2 na rana.

Da yake bayyana yadda lamarin ya faru, Dakta Moses ya ce, "Yan sanda dauke da makamai a cikin motoci shida wadanda aka rubuta "Intelligence Unit" kuma wadanda ke aiki a karkashin umarnin gwamnan jihar sun zagaye wani fili plot no 3 wanda aka fi sani da White House a kan titin Omerelu Street kusa da Salvation Ministries Headquarters, G.R.A da ke Fatakwal inda Shugabannin jihar da na kananan hukumomi na kungiyar magoya bayan Atiku (ASO) ke gudanar da taro domin gudanar da shirye-shiryen kamfe din PDP wanda za a gudanar a ranar 11 ga watan Fabrairun 2023.

"A lokacin da suka lura jami'an tsaron sun zo ne domin hana taron, sai wasu mahalarta taron suka ruga tare da tsallakawa ta wayar zagaye waje (barbed wire) hakan kuwa ya yi sanadiyyar jin raunukansu, a bangare daya kuma suka kama mutane sama da 30, shugabannin jiha da kananan hukumomi, mafiyawansu mata wadanda suka zuba su cikin motoci biyu suka tafi da su Intelligence Unit din, a yayin da motoci hudu kuma suka zagaye wajen taron."


Sakataren ya bayyana cewa duka nambobin wayar wadanda aka kama din basu shiga, inda ya yi kira ga gwamna Nyesom Ezenwo Wike da ya saki mambobinsu nasu nan take ya kuma kawo karshen irin siyasar da ya ke yi ta a mutu ko a yi rai a jihar tare da daina tunzura mutane kan magoya bayan na Atiku a jihar.

Sakataren, wanda ya bayyana cewa kuru'un jihar Ribas na Atiku Abubakar ne da PDP kawai, ya yi kira ga shugaban 'yan sandan Nijeriya da ya gaggauta bada umarnin sakin mambobin nasu, ya kawo karshen dambarwar siyasa a jihar ta Ribas domin kaucewa shekar da jini a yayin gudanar da zabe wanda gwamnan ya tunzura.

Ya dai bayyana cewa kowa na da hakkin a barsa ya yi zabinsa na siyasa ba tare da takurawa ba.

No comments

Powered by Blogger.