Header Ads

Kasar Pakistan ta rufe shafin Wikipedia saboda wallafa bayanan batanci

Shugaban Pakistan Dakta Arif Alvi

Kasar Pakistan ta toshe shafin Wikipedia saboda wallafa wasu bayanai na "batancin ga addini"

An bayyana matakin ne ranar Asabar bayan wa'adin - kwanaki biyu da aka baiwa shafin yanar gizon na encyclopedia ya cire wasu bayanai a shafin - ya cika.

Hukumar sadarwar kasar tace shafin na Wikipedia ya gaza bin umarnin da aka ba shi kafin cikar wa'adin.

Gidauniyar Wikimedia, wanda ke da mallakin shafin na Wikipedia, ya ce matakin toshe shafin na nufin haramtawa al'ummar Pakistan samun "ilimi kyauta daga katon rumbin ilimin."

Batanci ko sabo babban laifi ne da zai iya janwo rikici Pakistan.

A baya dai kasar - wadda ke da rinjayen musulmi - ta taba toshe wasu kafofin sadarwa kamar shafukan Tinder da Facebook da kuma Youtube.

Mai magana da yawun hukumar sadarwar kasar Malahat Obaid ya ce shafin na Wikipedia ya gaza daukar mataki a kan abubuwan da aka nusar da shi na "batanci."

"Sun cire wasu daga ciki amma ba duka ba" in ji shi, inda ya tabbatar da cewa shafin zai cigaba da kasancewa a rufe har zuwa lokacin da zai cire "duka abubuwan da aka nusar da shi a kan su"

To sai dai ba a yi cikakken bayani kan abubuwan batancin da shafin ya wallafa ba.

To sai dai gidauniyar Wikimedia ta ce idan haramcin ya cigaba hakan zai "hana kowa samun ilimi game da tarihi da al'adun Pakistan."

Masu fafutikar kare hakkin bil-adama sun bayyana damuwa game da matakin, suna masu cewa matakin "tamkar yunkurin samun iko ne ga abubuwan internet."

"Babban dalili shine saboda shirun da ake yi ne," in ji Usama Khilji wani mai sharhi game da shafukan internet.

"A lokuta da dama ana amfani da kalmar 'batanci' a matsayin kuntatawa mutane," in ji shi.

A shekarar 2012 Pakistan ta toshe shafin You Tube saboda karuwar "abubuwan sabo a shafin."

An kuma toshe shafin Facebook a shekarar ta 2010 bayan da aka yi ta samun gangamin kiraye-kirayen zana hotunan Annabi Muhammad (S.A.W) a shafin.

Haka kuma a bayan an toshe shafukan Tinder da Grinder sakamakon yada "abubuwan da suka saba wa addini" a kasar.

No comments

Powered by Blogger.