Header Ads

INEC ta fara horas da ma'aikatan wucin-gadi miliyan 1.2 domin aikin zaɓen 2023

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara aikin horas da ma'aikatan da za su yi aikin zaɓen 2023 a cikin Fabrairu da Maris.

Ma'aikatan na wucin-gadi su miliyan 1 ne da 265,227, kamar yadda Babban Jami'in Wayar da Kai kuma Kwamishina na INEC, Mista Festus Okoye, ya bayyana a ranar Litinin, a wurin bayar da wani horon a ranar Litinin.

Ya ce hukumar ta ɗauki wannan horaswa da muhimmanci, ganin cewa Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya sha alwashin tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe, karɓaɓɓe, kuma wanda jama'a za su yi tururuwar fita su jefa ƙuri'a.

Okoye ya ƙara cewa haka kuma wannan zaɓe mai zuwa, zaɓe ne wanda za a yi amfani da na'urar fasaha a wurin zaɓe.

Ya yi tsinkayen cewa aikin ofishin sa ne wanda aka ɗora wa haƙƙin shawartar Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi (REC) da jami'an zaɓe hanyoyin da su ka fi dacewa su fahimtar da jama'a batutuwan da su ka danganci amfani da na'urorin fasaha a lokacin zaɓe.

Ya ƙara da cewa a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris 'yan Nijeriya za su zaɓi shugaban ƙasa, sanatoci 109, mambobin majalisar wakilai su 360, gwamnoni 28, sai mambobin majalisar dokoki 993.

Ya ce mutum miliyan 93 da 469,008 ne su ka yi rajistar katin zaɓe, kuma ake sa ran za su fita su jefa ƙuri'a a ranakun 25 ga Fabrairu da 11 ga Maris.

Ya ce: "Zaɓen 2023 zai tafi ne a bisa tsarin amfani da na'urar fasahar zamani. INEC za ta yi amfani da na'urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, wato BVAS a dukkan rumfunan zaɓe 176,846 a ƙasar nan.

"Kuma INEC ta yi gwajin waɗannan na'urorin, wato BVAS ta tabbatar da ingancin su. Yanzu haka ana ci gaba da ba su lambobin tantance mai katin shaidar rajistar zaɓe, ta yadda za su kasance lambobin sun zama mabiyi da mabiyi, ko ɗaya bayan ɗaya a lokacin zaɓe."

A cewar Okoye, Sashen Dokar Zaɓe na 47(2) ya tilasta cewa babu wanda zai yi zaɓe ba tare da an tantance shi na BVAS ba.

Ya ƙara da cewa: "Za a yi amfani da baturen zaɓe 707, 384 da su ka haɗa da mataimakan su. Sai kuma wasu ma'aikata 17,685 a matsayin turawan zaɓe masu sa-ido, jami'an tattarawa da bayyana sakamakon zaɓe su 9,620, sai kuma jami'an tsaron rumfunan zaɓe su 530,538. Ya ce gaba ɗaya idan an haɗa, sun cika 1,265,227 kenan.

Dukkan waɗannan su na ci gaba da samun horon sanin makamar aiki, yayin da nan da 'yan kwanaki za a ci gaba da bayar da horon ga saura, inji shi.

No comments

Powered by Blogger.