Header Ads

Rashin tsaro: Rundunar mafarauta ta yi gargadi ga barayin daji


Mafarauta a yayin wani buki

A yayin da rayukan mutane ke ci gaba da salwanta a Nijeriya sakamakon rashin tsaro, na baya-bayan nan inda barayin daji suka kashe 'yan banga mutum 41 a jihar Katsina, babban kwamandan rundunar mafarauta mai fatan zama hukuma ba da jimawa ba a Nijeriya, Ambasada Osatimehin Joshua Wale, ya gargadi barayin dajin da cewa jami'ansu sun shirya tsaf domin sa kafar wando daya da su.

Osatimehin, wanda ya bayyana cewa su ma sun rasa jami'ansu mutum 81 a shekarar da ta gabata sanadiyyar barayin dajin, ya ce, jami'ansu suna cike da azama ta tabbatar da tsaro a cikin dazuka.

Kwamandan ya ce barayin suna amfani da muggan makamai, su kuwa ba ya yiwuwa su ruke irin su, domin kuwa har yanzu gwamnatin kasar ba ta kammala amincewa da su a matsayin hukuma ba.

Sai dai ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu kudurin kafa hukumar mafarauta ya tsallake tare da samun amincewar bangarori biyu na majalisun dokoki biyu na Nijeriya, yanzu sanya hannun shugaban kasa kawai yake jira ya zamo doka.

Saboda haka sai ya gargadi barayin dajin da masu satar mutane a kan su sani masu dazukan na asali sun kusa zuwa su mallake muhallansu na asali da aka san su da su shekaru masu yawa.

Amincewa dai da jami'an kungiyar mafarauta ta zamo cikin hukumomin tsaro kan iya nuna tasirin da za ta iya yi wajen samar tsaro ko akasin haka.

No comments

Powered by Blogger.