Header Ads

Mutane 146,913 ne daga ciki da wajen Nijeriya za su sa ido a kan zabe - Hukumar INEC

Shugaban INEC

Shugaban hukumar zabe ta kasa wato INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa mutane 146,913 ne daga cikin Nijeriya da kasashen waje za a baza domin sa ido a cikin zaben shugaban kasa da za a gudanar a cikin karshen mako.

Farfesa Mahmood ya bayyana haka ne a yayin wani taro da ya yi da wasu masu sanya idanun a ranar Talata a Abuja a yayin da zaben shugaban kasar da na gwamnoni ke kara karatowa a ranar 25 ga watan Fabrairun wannan shekara. 

Shugaban hukumar ya kara da cewa kamar yadda ake yi a duk duniya, mafi yawanci hukumomin zabe kan gayyato hukumomin da ke cikin gida da kasashen waje domin su zubo masu sa ido ko kuma su shirya tafiye-tafiyen karantar me masu kula da zabe ke yi.

Ya dai bayyana cewa wadannan masu sa ido kan yi rahoto su kuma bayar da shi a kan me suka ga ya yi daidai da kuma wuraren da ake da rauni a kan tafiye-tafiyen da suka yi, masu kula da zabe da sauran abubuwa.

Rahoton nasu, kamar yadda ya bayyana, za a yi amfani da shi ne wajen yin gyare-gyare domin a kara samun cigaba.

Farfesan a cikin jawabin da ya yi masu ya bukacesu da kada su yi shisshigi cikin al'amurra kuma kada su nuna bangaranci.

No comments

Powered by Blogger.