Header Ads

Sabuwar girgizar kasa a Turkiyya ta yi sanadiyyar rasa rayuka da raunata da dama

Wani yaro da ya sami rauni a sabuwar girgizar Kasar 

A ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, wata sabuwar girgizar kasa ta kara faruwa a kasar Turkiyya inda ta yi sanadiyyar rasuwar mutane 6 wasu kuma 294 suka raunata.

 Girgizar kasar mai karfin 6.3 ta ranar Litinin ta faru ne a birnin Defne a yankin Hatay da misalin karfe 8:04 na dare a bodar Siriya da Turkiyya, sati biyu bayan faruwar girgizar kasa wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 47,000 a kasashen biyu. 

Girgizar kasar an jiwo ta a kasashen Siriya, Lebanon, Jordan, Isra'ila da Misra kamar yadda kafar watsa labarun kasar Turkiyya, Anadolu news agency, ta bayyana, yayin da kafar watsa labarai ta Siriya, SANA, ta bayyana cewa mutane 6 sun jikkata sakamakon abubuwan da suka fado masu, yayin da gidaje da dama suka rushe, wasu da mutane a ciki a Hatay da ke Turkiyya kamar yadda magajin garin ya bayyana.

Zuwa ranar Litinin, yawan wadanda suka rasu sun karu zuwa 41,156 a Turkiyya kawai kamar yadda hukumar bayar da agaji ta bayyana, ana kuma sa ran yawan ya fi haka, a Siriya kuwa akalla mutane 6,000 suka rasu.

Gidaje kusan 385,000 ne suka rugurguje ko suka samu mummunar rushewa, mutane da yawa har yanzu ba a gansu ba.

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa za a fara gina gidaje 200,000 a cikin wata mai zuwa a yankuna 11 da girgizar kasar ta shafa.

No comments

Powered by Blogger.